✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallar Idi da ladubbanta

Sallar Idi da ladubbanta: Malamai sun hadu cewa ta kowane hali a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara kamar…

Sallar Idi da ladubbanta:

Malamai sun hadu cewa ta kowane hali a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara kamar yadda Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumi a ranar Sallah kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).

Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wanda suka fi kyau cikin tufafin mutum, a sa turare a fita masallacin Idi. An so maza da mata, manya da yara su tafi masallacin idi, amma a tsare ladubban fitar. Wato kada mata sun caba ado ko sun sanya turare kuma kada a rika cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari’a ta hana.

Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sanya a koma ga sabo, kada murna ta sa a aikata bidi’o’in da za su bata kyawawan ayyuka.

 

Daga cikin ladubban murnar Sallah akwai:

1. Taya juna murna da duk lafazin da ya sauwaka, kamar “Allah Ya karba mana” da makamancin haka. An ruwaito cewa wadansu daga magabatan kwarai sun aikata haka. Misali Jubairu bin Nufair ya ce, “Sahabban Annabi (SAW), idan suka hadu da juna sukan ce, “Allah Ya karba mana, Ya karba muku.” Imam Ahmad ya ce Isnadinsa mai kyau ne, sannan Hafiz ya kyautata Isnadinsa a cikin Fathul Bari (2/517), kuma a duba Tamamul Minnah na Albani domin karin bayani. Kuma an ruwaito Imam Ahmad yana cewa: “Ba zan fara fada wa mutum haka ba, amma idan ya fada min zan amsa.” Shi kuma Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (Rahimahullah) ya ce, “Fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umrni da ita ba, kuma ba a hana ba, wanda ya aikata, ya yi koyi, wanda ya ki, ya yi koyi.” Majmu’u Al-Fatawa (24/253). Hakika irin wannan gaisuwa tana yin tasiri wajen karfafa zumunta da ruhin soyayya a tsakanin Musulmi.

2.  Ziyartar ’yan uwa da makusanta da sada zumunta. Wannan mustahabbi ne a kowane lokaci, amma an fi karfafa shi a irin wannan lokaci, musamman ziyartar iyaye, domin ana sanya musu farin ciki, kuma haka cika umarnin Allah ne na a kyautata musu.

3. Wadata iyali da abinci da abin sha: Babu laifi a wadata abinci da abin sha a wadannan ranaku ba tare da almubzzaranci ba. Kuma ya hallata a yi wasannin da suke halal, saboda Hadisin Anas a wurin Abu Dauda da Nisa’i bisa Isnadi ingantacce da ya ce: “Lokacin da Annabi (SAW) ya isa Madina, ya iske su suna taruwa rana idoji, sai ya ce, “Kuna da wuni biyu da kuke wasanni a cikinsu, to, hakika Allah Ya musanya muku da mafiya alheri: Ranar karamar Sallah da Ranar Layya.” Kuma ya halatta a yi wake-waken da suke na halal, saboda Hadisin A’isha (RA) cewa, “Manzon Allah (SAW) ya shiga wurina ina tare da wadansu kuyangi biyu suna kida da waka (wasu sun ce da shantu ko kwarya), sai ya kishingida a kan tabarma ya juya fuskarsa. Sai Abubakar (RA) ya shigo ya yi min fada ya ce “Shaidan a gidan Annabi (SAW)? Sai Manzon Allah (SAW) ya kalle shi ya ce “kyale su – a wata ruwayar ya ce “Ya Abubakar kowadanne mutane suna da Idi, wannan Idinmu ne.”

 

Wasu bidi’o’i da ake yi lokacin bukukuwan Idi

1. Wadansu kan kirkiro ayyuka na raya daren Idi da ibada bisa dogaro da Hadisan da ko dai masu rauni ne ko na karya.

2. Ziyartar makabarta, wannan ya saba wa manufar Idi na nuna farin ciki da jin dadi, domin a cikin zuwa makabarta akwai jaddada bakin ciki, kuma hakan ya saba wa shiriyar Manzon Allah (SAW) da ayyukan magabata na kwarai. 

3. Cudanya tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwan Sallah. Wannan babbar fitina ce, mai hadari da ya wajaba shugabanni da malamai su hana, kuma ya kamata Musulmi manya da matasa su rika jira mata su bar masallatai kafin su tashi bayan idar da Sallah. 

4. Fitar mata sanye da turare kuma a cikin ado: Abin da ya zama wajibi shi ne iyaye da waliyan mata su rika umartar su da suturce jiki da sanya hijabi da lizimtar ladubban fita daga gida tare da gargadinsu su guji auka wa duk abin da zai fusata Allah. Idan ba za su tsare hukunce-hukuncen shari’a ba, to, wajibi ne su hana su fita gaba daya.

5. Sauraren haramtattun kade-kade da wake-wake, kila wadansu na iya fakewa da Hadisin kuyangi biyu su aikata abin da yake haram. Manzon Allah (SAW) ya ce, “Za a samu wadansu mutane a cikin al’ummata da za su rika halatta zina da alhariri da giya da wake-wake da kayan kade-kade.” Wake-wake da kayan kade-kaden da suka saba wa shari’a wajibi ne a guje musu.

6. Wasa da Sallah, cikin jama’a da yin barci ba a yi Sallah ba. Babban abin bakin ciki shi ne mutane da yawa suna wasa da Sallah a cikin jama’a ko su yi barci ba su yi sallar ba, saboda sun bata lokacinsu wurin hira ko wasanni sun gaji a ranakun Sallah. Don haka ya wajaba a ga kowane Musulmi ya tabbatar bai yi amfani da lokacin bukukuwan Sallar Idi domin aikata abin da zai fusata Allah Madaukaki ba.

Ya Allah! Ka tabbatar da mu a kan imani da aiki nagari, Ka rayar da mu rayuwa mai tsabta, Ka riskar da mu ga salihan bayi, Ka sanya iliminmu ya zamo don neman yadarKa da kusantarKa, mai amfanarwa ga bayinKa. Ka jibince mu a duniya da Lahira, kuma Ka shiryar da mu zuwa ga gaskiya da izininKa, lallai Kai Kana shiryar da wanda Ka so zuwa ga tafarki madaidaici.

Barka da Sallah!