✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samuel Eto’o ya koma Eberton

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Kamaru Samuel Eto’o ya koma kulob din Eberton da ke Ingila kamar yadda kulob din…

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Kamaru Samuel Eto’o ya koma kulob din Eberton da ke Ingila kamar yadda kulob din ya sanarwa duniya.
Kulob din ya ce Eto’o ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara biyu bayan ya bar kulob din Chelsea a kakar wasan da ta wuce.
Eto’o wanda ya taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka har sau hudu, ya zura wa Kamaru kwallaye 56 daga cikin wasanni 118 da ya yi mata.
dan shekara 33, ya yi wasa a kulob da dama da suka hada da FC Barcelona na Sifen da Inter Milan a Italiya da Real Mallorca da ke Sifen da Anzhi Makhachkala da ke Rasha kafin komawarsa kulob din Chelsea na Ingila a bara.
Musa Yahaya yana daga cikin ’yan kwallon  kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ’yan kasa da shekara 17 da suka lashe gasar cin kofin duniya da ya gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Nuwamban bara.