✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar acaba ta fi aikin gwamnati – Alhaji Ubale

Aminiya: Da farko zamu so ka gabatar da kanka? Alhaji Ubale: Sunana Alhaji Ubale Ahmed shugaban kungiyar ’yan acaba da Keke Napep reshen Jihar Bauchi…

Aminiya: Da farko zamu so ka gabatar da kanka?

Alhaji Ubale: Sunana Alhaji Ubale Ahmed shugaban kungiyar ’yan acaba da Keke Napep reshen Jihar Bauchi mun kafa wannan kungiya ne domin ganin mun wayar da kan matasa game da mahimmancin neman halal a tsakanin al’umma. Kuma wannan kungiya muna mata lakabi da suna Acomoran muna da dimbin matasa wanda suke sana’ar acaba a daukacin wannan jihar.
A dokokin wannan kungiya bama fita mu kama dan acaba kamar yadda wasu kungiyoyi suke yi a Bauchi duk wanda ya ke bukatar shiga kungiyar zamu masa rijista sannan kuma mu fada masa kadan daga cikin dokokin kungiyarmu.
Aminiya: Wane lokaci aka kafa wannan kungiyar?
Alhaji Ubale: An kafa wannan kungiyar sama da shekara 30 da suka gabata kuma muna da mambobi masu yawa wasu ’yan Jihar Bauchi ne wasu kuma sun fito daga jihohin daban-daban sannan kuma bama wa ’yan shaye-shaye rijista.
Aminiya: Mambobinka sun kai mutum nawa a jihar Bauchi?
Alhaji Ubale: Muna da mambobi zalla ’yan acaba sama da dubu shida sannan kuma akwai masu tuka Keke Napep suma suna da matukar yawa saboda haka ina alfahari da wannan sana’a ta acaba domin duk wanda yake sana’ar ya wuce ya je ya zauna a kofar gidan dan siyasa yana jiransa.Wannan kungiya tana da zama ne a cikin tashar motar Yankari da ke kan hanyar unguwar Jahun a cikin garin Bauchi mun kuma shafe sama da shekara da shekaru muna zaune a cikin tashar sai dai kuma muna da wasu rassa a cikin jihar. Da yawa daga cikin wadanda suke wannan sana’a na achaba sun shiga aikin ne sakamakon matsalolin rayuwa wani yana da mata biyu da yara sama da 20 wani kuma sabon aure ne, amma ba ya da aikin yi don haka wajibi ne ya rike sana’ar hannu biyu domin ita ce mutuncinsa.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga Sabon Shugaba Muhammadu Buhari?
Alhaji Ubale: Abin da nake so sabon shugaban kasa ya yi ga ’yan acaba shi ne ya farfado mana da kananan masana’antun da suka kwanta dama sakamakon sakacin gwamnatocin baya. Lokacin da ya zo Bauchi kamfe sai da ya yi kuka sakamakon yadda ya ga dimbin matasan da suke binsa a baya, amma ba su da aikin yi. Sannan muna son ya fito mana da wani tsari na kyautata rayuwar ’yan achaba a duk inda suke a fadin Najeriya. Kuma idan ka duba sosai a shekarun baya da suka wuce jihohi da dama sun haramta sana’ar achaba abin da ya sa haka shine babu hannun Gwamnatin Tarayya ne duk wanda ya kammala karatu babu abin da yake so sai aikin gwamnati. Ka ga ya kamata sabuwar gwamnati ta fitar da wani tsari duk lokacin da za ta dauki sabbin ma’aikata ta rika daukowa daga kananan kungiyoyi irin namu domin mu ne muka san cutar da ke damun matasan Najeriya.
Aminiya: Mene ne sakonka ga mambobin kungiyarku?
Alhaji Ubale: Babban sakona ga mambobin wannan kungiya shi ne don Allah su ci gaba da bin dokokin tuki a duk lokacin da suka hau kan hanya domin hanya ba ta mutum daya ba ce. Babu abin da yake da wahalar tafiyarwa kamar shugabanci kowa da abin da yake so shugaba ya yi. Kashi 85 cikin 100 na wadanda suke sana’ar achaba suna yi ne sakamakon kuncin talauci da rashin aikin yi wanda ya addabi matasan Najeriya, amma yanzu muna ganin abubuwa za su daidaita tun da an samu sabuwar gwamnatin talakawa. Hakazalika, ba mu ji dadin yadda tsohuwar gwamnati ta gagara magance matsalar karancin man fetur ba a kasar nan duk da cewa Allah Ya albarkaci kasar da mai.
Aminiya: Wane sako kake da shi ga matasan Jihar Bauchi?
Alhaji Ubale: Babban sakona ga matasa shi ne kowa ya kama sana’a sannan kuma a rika hadawa da zuwa makaranta babu wata al’umma da za ta samu ci gaba, sai tana da matasa masu ilimi da sanin ya kamata. Kuma ina fatar alheri ga daukacin ’yan Najeriya bisa yadda ake bikin rantsar da sabuwar gwamnati wadda muka zaba kuma zamu ci gaba da addu’o’i na musamman Allah Ya ba su damar cika alkawurran da suka dauka a lokacin kamfe. Kamar yadda kowa ya sani ne ina alfahari da sana’ar achaba kuma wannan sana’a ya fi aikin gwamnati rufin asiri. A rayuwa akwai da dama daga cikinmu wanda suka mallaki gidaje ta sanadiyyar sana’ar wadansu kuma har sun kai ga sauke farali.