✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sarakuna 3 ne kadai ba su da hannu a matsalar tsaron Zamfara’

A makon jiya ne kwamitin da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawalle ya kafa domin binciko abin da ke haddasa kashe-kashen da jihar ta tsinci…

A makon jiya ne kwamitin da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawalle ya kafa domin binciko abin da ke haddasa kashe-kashen da jihar ta tsinci kanta ciki ya mika rahotansa ga gwamnati.

Kwamitin a karkasahin jagorancin tsohon Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Muhammad D. Abubakar ya bukaci a kori sarakuna biyar da uwayen kasa 33 da kuma hakimai da dama.

Sai dai wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa sarakunan da ake zargi da hannun a sha’anin kashe-kashe da satar shanu a jihar sun zarta abin da kwamitin binciken ya nuna nesa ba kusa ba.

“Su kwamitin binciken sun ce a sauke sarakuna biyar, to amma ina tabbatar maka cewa a cikin sarakuna 17 na wannan jiha ta Zamfara, sarakuna uku ne kadai bincike ya tabbatar da ba su da wata alaka da wannan lamari,” inji shi.

Shugaban Kwamitin, Alhaji Muhammad Abubakar ya ce kwamitin nasa ya mika bukatar warware rawunan sarakunan ne bayan da ya same su da hannu dumu-dumu cikin lamuran rashin tsaron da ya addabi jihar shekara da shekaru.

Akwai ma wurin da kwamitin ya ce wadansu daga cikin tubabbun ’yan bindigar da suka gana da su a lokacin zaman da suka yi da masu ruwa-da-tsaki, suka shaida musu cewa wadansu sarakunan na da hannu wurin tilasta musu daukar makamai.

Kwamitin ya bukaci gwamnati ta yi wa tsarin masarautun jihar garambawul, yana mai cewa sarakunan jihar sun zama tamkar maroka a hannun al’ummomin da suke mulki a jihar.

To sai dai kwamitin ya bukaci a ba wadansu daga cikin sarakunan lambar yabo saboda yadda suka jajirce wajen tabbatar da doka da adalci a masaurutunsu. Kuma akwai ’yan sanda da sojoji da ma’aikatan gwamnati da kwamitin ya bukaci a kore su daga aiki, baya ga wadanda ya ce a yi musu karin girma saboda kokarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kafin gabatar da rohoton, wani malamin addinin Musulunci mai suna Dokta Aliyu Jangebe ya yi shagube ga masu rike da sarautun gargajiya a wajen wani taron masu ruwa-da-tsaki kan al’amuran tsaron jihar; inda ya rika ba da misali da wani Bafulatani da aka tilasta wa sayen filayensa da ya mallaka har sau biyu bisa zalunci.

Ko a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari, an kori hakimai da uwayen kasa da dama a wani mataki da ba kasafai gwamnatin kan dauki irinsa ba.

Kuma a watan Agustan bana, an sauke tsohon Sarkin Maru, Alhaji Abubakar Cika Ibrahim daga sarauta, bayan da wani kwamiti ya gano cewa yana da hannu a kashe-kashe da satar shanu a Jihar Zamfara.

Sarkin na Maru ya gamu da fushin jama’ar masarautarsa ce bayan da ya tafi garin Kanoma, inda Gwamna Matawalle ya je ziyarar jaje ga jama’ar garin, sakamakon harin ’yan bindiga da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a watan Yunin da ya gabata.

A lokacin, jama’ar sun yi kokarin far wa Sarkin, ba domin Allah Ya sa Gwamna ya shiga tsakaninsu ba, da mutanen masarautar sun yi masa ha dadi, shi da uban kasar Kanoma.  Kuma ba tare da bata lokaci ba Gwamnan ya kafa kwamitin bincike ina aka same shi da laifi, kuma Gwamnan ya cire shi daga sarauta.

Jama’ar jihar da wakilinmu ya tattauna da su kan lamarin, sun bayyana goyon bayansu kan duk mataki da gwamnati za ta dauka a kan wadanda suka kira da maciya amanar a’lumma.

“Babu yadda za a yi a ce kai da aka ba amanar jama’a, kai ne kuma za a same ka da hannu wajen tayar da hankalinsu. Wannan ba karamin rashin tausayi ba ne kuma ya kamata gwamnati ta hukunta masu hannu a musguna wa al’umma. Kuma wallahi duk wanda ya nemi ya yi amfani da karfin fada-a-ji, don ya hana a hukunta wadannan mutane, shi ma zai dandana kudarsa. Domin sai an dauki matakin ba-sani-ba-sabo a kan maketata ne kadai zai zama izina ga masu son cin amanar jama’a,” inji wani mazaunin Maru mai suna Usman Haruna.

Shi ma wani mazaunin Gusau mai suna Habibu Isah, ya shaida wa wakilinmu yadda masu sarautun gargajiya suke amfani da matsalar tsaron jihar suna muzguna wa jama’arsu a tsawon lokaci.

“Idan ka shiga garuruwa da kauyukan da wadannan mutane ke mulki, za ka ga tsantsar yadda sarakuna da hakimai ke zaluntar jama’a. Idan kana so ka tabbatar da haka, wata rigima da ta shafi fili ko gona ta hada ka da wani sannan za ka ga tsabar rainin wayo da zalunci,” inji shi.

Adamu Danhassan cewa ya yi, wani lokaci tilasta wa masu rike da masaurutun gagarjiyar ake yi, suna shiga harkar satar shanu kuma dole ce ta sa suke ba masu yin satar shanun ko kuma ’yan bindiga hadin kai.

“Dalilin da ya sa na ce haka shi ne, a bara ’yan bindiga sun zo sun kashe uban kasar Kucheri da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Rahotanni sun ce wani mutum ne ya je ya tsegunta wa ’yan bindigar wasu kalamai da uban kasar ya yi, a wajen wani taro kan sha’anin tsaro a fadarsa. Don haka ka ga su ma suna cikin tsoro ne.

Kuma baya ga wannan, akwai gundumomi da kauyuka da yawa da a wancan lokacin ba hannun gwamnati suke ba. Saboda haka ba su da yadda za su yi, illa su yi biyayya ga ’yan ta’addan, don gudun abin da zai je ya zo,” inji shi.