✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Charles III ya tabbatar da Rishi Sunak a matsayin Firaministan Birtaniya

Rishi Sunak shi ne Firaministan Birtaniya na 57 a tarihin kasar.

Rishi Sunak ya zama sabon Firaminista Birtaniya bayan da Sarki Charles III ya tabbatar da shi tare da ba shi izinin kafa gwamnati.

Hakan ya tabbata ne a ranar Talata bayan ganawarsa da Sarki Charles din a Fadar Buckingham.

Wannan ne dai nadi na farko da Sarki Charles na 3 ya jagoranta la’akari da cewa Sarauniya Elizabeth ce ta tabbatar da nadin Liz Truss kwanaki kalilan gabanin mutuwarta.

A jawabinsa na farko bayan tabbatar da shi a matsayin Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ya sha alwashin gyara kurakuran da aka tafka wadanda suka kai kasar ga fada wa halin matsananciyar matsalar tattalin arziki.

Jim kadan bayan tabbatar da shi, Rishi Sunak ya ce aiki na farko da zai sanya a gaba shi ne samar da sauye-sauye don gyara ga kura-kuren da aka tafka cikin makonni bakwa na mulkinta Truss lamarin da ya durkusar da tattalin arziki.

A cewarsa baya zargin Truss kuma matakan da ta dauka ba gazawa ba ce, haka zalika bada mummunar manufa ta samar da sauye-sauyen da suka ill aga tattalin arziki ba, hasalima tsari ne mai kyau sai dai sun juye zuwa matsala ne saboda halin da duniya ke ciki.

Rishi Sunak mai shekaru 42 wanda mabiyin addinin Hindu ne dan asalin kasar Indiya, ya zama shi ne Firaministan Birtaniya na 57 a tarihin kasar.

Kuma shi ne Firaminista na uku da ya shiga Fadar Downing Street a wannan shekarar, sannan mafi kuruciya a cikin firaministocin da suka mulki kasar a shekara 20 da suka gabata.