✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Gombe ya gina asibiti na miliyoyin Naira a Gombe

Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya gina wa al’ummar yankin Bolari ta Yamma da ke fadar Jihar Gombe asibitin zamani na…

Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya gina wa al’ummar yankin Bolari ta Yamma da ke fadar Jihar Gombe asibitin zamani na miliyoyin Naira.

Sarkin wanda ya yi fice wajen gudanar da ayyukan alheri ga al’ummarsa tun hawansa karagar mulki a matsayin Sarki na 11, ya fara tallafa wa talakawansa ne musamman  ’ya’yan ’yan gudun hijira da marasa galihu wajen sanya su a makarantun boko don samun ilimin zamani.

A shekararsa ta farko a karagar mulki ya sanyayara ’yan gudun hijira fiye da dubu uku a makarantun firamare da kuma daukar nauyin karatunsu.

Unguwar Bolari ta Yamma ba ta da asibiti sai da Sarkin ya gina musu. Asibitin ya kai matakin kammalawa da 95 cikin 100, kuma jami’an gudanar da aikin sun ce da zarar an kammala za a fara aiki da shi.

A shekarunsa hudu a gadon sarauta Sarkin ya zama abin misali a tsakanin sarakunan Najeriya da na Afirka wajen aiwatar da ayyukan ci gaba ga talakawa a fannonin rayuwa daban-daban.

Wakilinmu ya zanta da wadansu mazauna Unguwar Bolari, inda suka nuna jin dadinsu sannan suka yi wa Sarkin addu’o’in fatan alheri tare da bayyana shi a matsayin Sarki mai taimakon talakawansa.

“Mu talakawa tsakaninmu da Mai martaba Sarkin Gombe abin ya wuce godiya sai dai kawai mu yi ta addu’ar Allah Ya kara wa Sarki lafiya da nisan kwana ya kuma shige wa Sarki gaba a dukan lamuransa,” inji su.

Sarkin ya gina makarantun Islamiyya da masallatai da dama, sannan ya samar da ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa ga al’ummarsa a sassan garin Gombe.