✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi addu’ar cikar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shekara 1 a kan mulki

Yadda aka gudanar da addu'ar cikar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shekara daya a bisa mulki.

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jagoranci addu’a ta musamman domin murnar cikarsa shekara guda a kan karagar mulkin Masarutar Kano.

Addu’ar ta musamman ta gudana ne a Babban Masallacin Kano a safiyar Talata, 9 ga Fabrairu, 2021.

Aminiya ta halarci addu’ar, ga kuma kadan daga cikin hotunan da ta yi muku tsaraba kafin karin labarin ya biyo baya.

Sarki Aminu Ado Bayero da ‘yan fadarsa a yayin addu’ar cikirsa shekara daya a kan mulki da aka gudanar a Babban Masallacin Kano. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Sarki Aminu Ado Bayero, sanye da farin rawani a lokacin addu’ar da ta gudana a ranar Talata. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Wani sashe na fadawa da mahalarta taron addu’ar cikar Sarki Aminu Ado Bayero shekara daya a kan mulki ranar Talata, 9 ga Maris, 2021. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Sarki Aminu Ado Bayero na fuskantar ‘yan fadarsa a lokacin addu’ar. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Lokacin da ake shefa addu’ar bayan kammala zaman. Hoto: Sani Ibrahim Paki.

Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano na 15 daga gidan sarautar Sullubawa kuma an haife shi ne a ranar 1 ga watan Yuli 1961.

Ya hau karagar mulkin Masarautar ne a ranar 9 ga watan Maris, 2020, bayan Gwamantin Jihar Kano ta sauke Sarki Muhammadu Sanusi II.

Kafin zamansa Sarkin Kano, shi ne Sarki na Farko a Masarautar Bichi, wanda bayan saukarsa, dan uwansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero ya zaman Sarkin Bichi.

Mahaifinsa shi ne Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero, wanda Allah Ya yi wa rasuwa yana da shekara 83 a ranar 6 ga watan Yuni, 2014 bayan shekara 50 a kan gadon mulki. Ana ganin Sarki Ado Bayero ake kuma ganinsa a matsayin sarki fami kima a zamanin mulkinsa.

Mahaifiyarsa ta fito ne daga gidan Sarautar Ilori a Jihar Kwara, kuma ya rike wasu sarautu a lokuta daban-daban kafin zamansa Sarkin Kano.