✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar mutane: Kalaman Sarkin Muri sun bar baya da kura

Sarkin ya ba Fulani ’yan Bororoji wa'adin kwana 30 su fice daga kasarsa.

Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njidda Tafida ya bai wa Fulani ’yan Bororoji wa’adin kwana Talatin su fice daga kasarsa.

Basaraken ya zargi makiyayan da yin garkuwa da mutane a kasarsa, sannan ya kuma kausasa harshe cewa daga yanzu jama’ar masarautar za su dauki mataki a kan masu sace mutanen.

“Don haka, duk wani Bororo a kasar nan daga yau ya kirga, na ba shi kwana 30, idan an ci gaba da zuwa gari a kama mu a kashe, ku kuma ba ku fito kuka tsaya kuka yi fada da wanda yake yi ba, to mu kuma za mu ja layi,” inji shi.

A cewarsa, muddin ’yan Bororojin suna son zama a yankin Muri to  ya zama dole su daina sace masa mutane.

Sarkin ya bayar da umurni ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummarsa a lokacin da suka kai masa gaisuwar Babban Sallah a fadarsa da ke Jalingo.

Ya jaddada cewa ba zai bari a rika sace al’ummarsa, saboda haka dole ne shugabanin Fulanin su hana yaransu shigowa garuruwa sana sace mutane har da mata.

Ya ce, “Babu yadda za a yi [mu bari] wani shege ya zauna a daji ya dauki matanmu ya zo ya yi zina da su.”

Alhaji Abbas Njidda Tafida ya ce abin bakin ciki ne ganin yadda miyagun suke sace mata suna musu fyade karfi da yaji.

A cewarsa, shugabanin Fulani sun san bata-gari daga cikinsu, don haka dole ne su tashi su hana su aikaya miyagun ayyukan.

Basaraken, ya kuma shawarci jama’a da su fito su kare kansu ta hanyar fuskantar masu garkuwa da mutane a duk lokacin da kai hari domin satar mutane.

Kalaman sarkin sun tayar sa kura a Najeriya inda satar mutane ta yi kamari har a Jihar Taraba da wasu sassan kasar inda ’yan bindiga suke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Wani rahoto da kamfanin bincike kan tsaro a Najeriya, Beacon Consulting, ya ce akalla mutum 1,031 ne aka kashe a Najeriya a cikin watan Yuni, baya ga daruruwan mutane da aka yi garkuwa da su.

Sarki ya tayar da kura

Wani mazaunin garin Jalingo, ya ce sarkin ya ce Sarkin ya yi jawabin ne cikin bacin rai saboda yadda matsalar garkuwa da mutane ta yi kamari a yankin.

A cewarsa, masu garkuwar suna cin karensu babu babbaka ta yadda suke sace yi wa mata fyade suke sace mutane sai an biya miliyoyi kafin su sake su.

“Sai su shigo da makamai su kwashe mutane yadda ka san su kadai ke da kudin sayen makamai,” inji Isa Ibrahim.

Muhammad Yusuf ya ce kalaman sarkin ba su dace ba, “domin tamkar yana ce wa mutane su far wa makiyaya ne babu gaira, babu dalili”.

Sarki bai yi magana ba

Wani masanin harkar tsaro mazaunin Abuja, Kabir Adamu, ya bayyana wa Aminiya cewa, bayanan basaraken ya dace da alkaluman da hukumomi da kuma binciken.

Don haka ya ce, sarkin yana da hujja ko da yake doka ba ta ba shi hurumin bayar da wa’adin ba.

Ya bayyana cewa, “Ko da sarki bai fito ya yi wannan kira ba, mutane za su kare kansu.”

Amma ya yi togaciya game da shawarar sarkin da ta dace da kiran da gwamnati da hukumomin tsaro ga jama’a cewa su kare kansu ta hanyar yin fito-na-fito ’yan bindiga.

“Hukuma ita ke da wannan hakkin, duk da cewa kusan ta gaza a wannan yanayin, mafita ba shi ne al’umma su kare kansu ba,” kamar yadda ya bayyana.

Ya ce abu ne mai wuya farar hula da ba shi da komai ya tunkari mutanen da ke amfani da bindigogin AK-47 dauke da kwanso biyu na albasurai kuma kowane na dauke da harsasai 60.

“Kai da ba ka da komai sai sanda ko wuka ka je ka tunkari wanda ke da bindigar da a cikin minti daya yana iya sakin albarusan — ka ga zai yi wuya a ce ka iya kare kanka a irin wannan yanayi.”

Ya bayyana cewa idan har ana so mutane su kare kawusansu to dole sai an ba su izini su mallaki makamai.

Sarkin ya yi kasada

Amma ya ce kalaman sarkin na iya jefa shi da mutanensa cikin hadari saboda “A baya wandanda suka bayar da irin wadannan wa’adin, sai muka ga barayin sun kai musu hari, wani lokaci ma har da kashe su.

“Abin da muke ji masa tsoro ke nan, idan bai samu kariya daga jami’an tsaro, wadanda suke da hurumin bayar da irin wannan wa’adi da shiga daji —kuma ba su yi ba”.

Daukar doka a hannu

Amma ya ce kalaman na iya sa mutane daukar doka a hannunsu a kan makiyayan da babu ruwansu.

Ya bayar da misali da Jihar Zamfara, inda ya ce a farko-farkon mastalar da aka samu, Jihar “ta kafa ’yan sa-kai, sai suka rika daukar doka a hannunsu, idan suka ga Fulani makiyaya da matansu sun shigo gari sai su kai musu hari, wani lokaci ma har da abubuwan da ba a iya fadi.

“To shi ne kusan ya kara assasa matsalar, su kuma Fulani da suka ga haka, sai suka fara neman makamai don su kare kansu.”