✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saukin mallakar bindiga a Amurka ke janyo asarar rayuka

Dokar Amurka ta bai wa ‘yan kasar damar mallakar bindiga, muddin ka cika sharudan da dokar kasar ta shinfida, wadanda ba su da tsanani. Sayar…

Dokar Amurka ta bai wa ‘yan kasar damar mallakar bindiga, muddin ka cika sharudan da dokar kasar ta shinfida, wadanda ba su da tsanani.

Sayar da bindiga a Amurka tamkar yadda za ka shiga shagon sayen wayar ne. Gasu nan baje,  ka  zabi wanda kake so kuma dai-dai kudin ka.

Sai dai duk wanda ya saya, akwai cikakken bayanansa a wajen masu sayarwa da gwamnati, domin gudun bacin rana.

Sai dai sama da shekara 10 zuwa 20 da suka gabata, an sha samun kashe-kashen mutane bakartai ta hanyar anfani da bindiga ba bisa ka’ida ba.

A wannan shekarar kawai, an yi asarar rayuka kusan 208.

Kila saboda hakan ne, kafin saukar  shugaba Barrack Obama ya yi kokarin ganin an tsaurara dokokin ko kuma sharudan mallakar bindiga, amma hakar ba ta cimma ruwa  ba.

Wani binciken da wata jarida a nan Amurka mai suna Usa Today, ta gabatar, ta gano cewa daga  shekarar 2006 zuwa yau, an kai harin  bindiga har sau 358, kuma mutane 1,883 ne suka yi hasarar rayuwarsu. Kuma wadannan kashe-kashen sun auku ne a jihohi 45.

kashe mutane a cikin taro ya auku sau uku a cikin shekarar 2017, inda mutane kusan 133 suka mutu, wato  na Les begas, sai  na Orlando da wanda aka yi kwana-kwanan a Tedas.

Binciken kuma ya gano daga bayanan da hukumomin gwamnati har ma da manema labarai ke  bayar wa game da kashe-kashen mutane da bindiga bai kai ainihin adadin abin da ke faruwa ba. Domin wasu ‘yan sanda ba su sani, ko sun sani kuma ba kasafai suke sanar da duniya ba, suma  manema labarai ba kowane kisa da bindiga suke samun labarin ba.

Binciken ya tabbatar da cewa kusan duk mutuwar da ake yi a Amurka, musamman na cikin taro da bindiga ake amfani.

Wani binciken wata kungiya mai zaman kanta da ke Amurka da ake kira Cann Communication ya nuna cewa, ana kashe mutane akalla  sau daya  a cikin mako biyu ta hanyar amfani da bindiga.

To sai dai kashe jama’a cikin taro irin wanda aka yi a kwana-kwanan a Les begas, Orlando, San Bernadino, Cali, da New Town su ne wadanda suka fi daukar hankali, a duniya baki daya.

Sau tari, abin da ke haifar da wannan kisar gillar, wani  binciken ya nuna cewa matsalar da ke  da alaka da batun cikin gida ne, musammam akan mace da namiji ko  kuma  batun da ke da  alaka da aure ko kuma samartaka da ire-iren su.

kuma daga cikin dukan kashe-kashen, kashi 19 ne kawai aka yi  a bainar jama’a, sauran duk  a gida ne ake aikata su. Daga cikin kashi 57 na wannan kashe-kashen kuma, za ka ga wadanda aka masu kisan sun san wadanda suka kashe su, duk kuwa saboda mallakar bindiga baida wahala ne yasa ake samun yawaitar hakan.

Shi dai kisan da aka yi na kwana-kwanan nan a Tedas, binciken da ‘yan sanda ke yi  ya gano cewa dan bindigar mai suna Debin Kelley dan shekara 26, ya shiga Majami’a ne ranar Lahadi  cikin bakaken kaya, kuma sai da ya kai tsakiyar wajen ibadaa, sai ya shiga harbi.

An jiyo Freeman Martins na hukumar kiyaye hadura na Jihar  ta Tedas, yana cewa a bincikensu,  sun gano cewa Kelly na da jikakka da surukarsa, kuma  wannan Majami’ar take zuwa  ibada. Sai  dai ranar da ya aikata wannan danyen aikin ba ta zo ba.

Don haka a cewar Martins wanna kisan ba ya da nasaba da  bambancin launin fata  ko  kuma addini.

Shi dai Kelly ko kafin ya aikata wannan danyen aikin, tsohon soja ne da aka kora a shekarar 2012 sakamakon cin zarafin matarsa da dansu guda daya, wannnan ya sa aka kore shi daga aikin soja,  kuma an ba shi takardar mummunar shaida game da aikin sojan da ya yi, tare da yi masa daurin  talala har na tsawon wata 12.