✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SEMA ta raba kayan Tallafi ga wadanda rikici shafa

Hukumar Ba Da Tallafin Gaggawa ta Jihar Kaduna SEMA ta raba kayan tallafi ga wadanda suka rasa dukiyoyinsu a lokacin rikicin Kasuwar Magani. Shugaban SEMA…

Hukumar Ba Da Tallafin Gaggawa ta Jihar Kaduna SEMA ta raba kayan tallafi ga wadanda suka rasa dukiyoyinsu a lokacin rikicin Kasuwar Magani.

Shugaban SEMA Ben Kure ne ya mika tallafin ga Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kajuru Suleiman Gambo Maro a sakatariyar karamar hukumar.

Ya kuma shawarci jama’ar karamarý hukumar, musulmi da kirista da su zauna da juna lafiya ta hanyar kaucewa duk wani abu da zai kawo sabani a tsakaninsu. Ben Kure ya ce Kasuwar Magani gari ne da ya yi fice wajen samar da amfanin gona, amma yanzu ya zama garin rikici da zubda jini babu gaira babu dalili.

“Bai da ce a ce Musulmi da Kirista suna fada da juna ba kasancewar duk Allah daya ne Ya halicce mu. Sannan kuma rikici baya kawo cigaba ga al’umma sai dai hasarar rayuka da dukiyoyi da kuma nadama daga baya. Saboda haka ya kamata mu daina fada da juna,” inji shi.

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Sulaiman Gambo Maro ya bayyana rashin jin dadinsa a kan kona Kasuwar Magani da aka yi a lokacin rikicin, wanda ya ce yana daya daga cikin hanyoyin samun harajin da karamar hukumar ke takama da su. Ya ce hakki ne na iyaye su sanya ido a kan irin abokan da ‘ya’yansu ke abota da su.