✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shagalin Ma’aurata lokacin bikin Sallah

Assalamu alaikum makarantanmu, ga bayani kan abubuwan da ma’aurata za su yi don dadadawa da kuma shagaltar da junansu a lokacin shagalin karamar salla. Da…

Assalamu alaikum makarantanmu, ga bayani kan abubuwan da ma’aurata za su yi don dadadawa da kuma shagaltar da junansu a lokacin shagalin karamar salla. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani amfanar da ma’aurata, amin.
Ranar shagalin sallah rana ce ta murna da farin ciki da sabunta kaunatayya, soyayya da zumunci tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki. Ma’aurata sai ku yi amfani da wannan lokaci na farin ciki don inganta dangantakarku da kara dankon kauna da soyayya, ya kasance kun kara shiga cikin ran juna sosai a wannan rana ta idin karamar Sallah; watau ku shagaltar da juna cikin shagalin sallarku sai ya zama kun hada dadi biyu kun bar sauran jama’a da daya. Ga hanyoyin da ma’aurata za su yi hakan:
1.      Ku Shagaltar Da Juna Da Kyautar Kyautata Soyayya:
Kyauta wata hanya ce mai kyau ta bayyana so, kauna da kulawa tsakanin mutane, musamman masoyan juna; Ranar sallah rana ce da kowa ke son ya ga ya kyautata wa mafi kusanci gare shi; don haka ma’aurata su yi amfani da wannan dama su ba junansu kyauta mai armashi, mai sa jin dadi a zuciya da sahihin murmushi a fuska.
•       Maigida sai ya yi wa uwargidansa kyautar abin da ya san ta fi so, ko abin da ya san tana mafarkin mallaka, to sai ya ba ta kyautarsa. Misali, maigida ya sa a shirya masa kek na musamman, wanda aka rubuta wasu kalaman soyayya a kai: kamar a rubuta “ke ta musamman ce a gare ni” ko ya ba ta kyautar zobe kuma ya sanya mata shi da kansa cikin yatsanta, ko wani abin hannu mai matukar kyau, ko wani kayan aikin girki ko na gida da ya san tana da bukata; ko dai wata kyauta komai kankantarta wacce za ta bayyanar da kauna da matsayinta a wajensa.
•       Uwargida ke ma sai ki zaba wa maigidanki irin abin da ki ka san yana matukar so; abin da kike ganin zai sa ya ji dadi sosai kuma ya yi farin ciki, ko da kuwa kudi ne ko wani abu daban, in dai zai kayatar da shi to shi za ki ba shi. Sai ki kawata kyautar taki, in wacce za a iya rufewa cikin takarda mai walkiya ne sai ki rufe, ki dan hada da ‘yar takarda mai dauke da kalaman nuna kauna, godiya da jin dadin zama da shi.
2.      Ku sabunta kaunarku!: Ranar yammacin Sallah, ko da daddare, sai ma’aurata su mayar da shi niyyar yin wani abu don sabunta so, kauna da kulawar da ke tsakaninsu ta yadda za su ji kamar ranar ne suka fara son juna, su yi kokari su dawo da soyayyarsu ta samartaka da ta amarci; misali, maigida ya yi wanka, ya ci gayu ya fesa turare, ya yi kamar zai je hira ne wajen masoyiyarsa, in ma da hali ya yi shiga irin wacce yakan yi lokacin samartakarsu, ita ma uwargida ta yi irin haka, su zauna su sha hirarsu cikin annashuwa da tsokanar juna, suna yi suna dan tsakurar wani kayan makulashe; ko dai ma’aurata su yi duk wani abu na sabunta soyayya da suka ga ya yi daidai da su da kuma irin yanayin da suke ciki.
3.      Daren shagalin kauna: ‘Ibadar Aure’ ita ce babbar ginshikin da aka gina auren gaba dayansa  a kai, amma al’adantar da ibadar aure da yawanci ma’aurata ke yi, da rashin sabunta shau’uka da yanayin gabatarwa a-kai-a-kai na sa ibadar aure tsakanin ma’aurata ta sallamce. Kamar yadda komai ya samu kulawa ta musamman a dalilin murnar Sallah karama, to a wannan daren Sallah sai ma’aurata su yi shirin ba ibadar aurensu wata kulawa ta musamman, su garwaya dukkan wasu shau’uka kyawawa masu alfanu da za su kara dandanon ibadar aurensu, a yi shiri na zuciya, a gyara jiki shi ma shimfidar auren a yi masa shiri na musamman. Uwargida ki yi gyara na musamman ga dakin aurenku ki kawata shi, in da hali ki samu zanen gado na siliki ki shimfida; ki sanyaya dakin da turare mai laushin; ki kashe fitilun dakin, ki kunna kyandir guda biyu don za su ba dakin yanayin kaunatayya. Wajen gabatarwar ibadar aure a ranar ku kai makura wajen burge juna, a jefar da duk wata kunya ko wani dalilin da zai kawo tsaiko, kuma a cire duk wani shamaki, ku wuce iyakarku ta al’ada a  wannan dare, ku ba juna daren da za ku dade  kuna murmushin dadi duk lokacin da kuka tuno da shi.
4.      Ku shagalar da juna cikin wasikar kauna: Zama za ki yi, ki tsara tsantsararriyar wasika zuwa ga maigidanki; wasikar tana iya kasancewa ta soyayya, ta godiya, ko ta yabo, ko ma ki hada duka cikin wasika daya. Ki cika ta da kalamai na so da kauna masu dadi, ki yabe shi yabo na gaskiya, kuma ki gode masa isasshiyar godiya, musamman idan kika duba irin dawainiyar da ya sha ta saye-sayen kayan sallah da na kuma hidimomin azumin da ya wuce. Sannan in da hali ki yi amfani da fensiri mai kala ki zana furanni masu kyau cikin wasikar, ki kawata su kuma ki dan sassaka wasu kalaman soyayya a ciki, kamar dai irin yadda ake yi wa saurayin da ake so a shekarun da rubutun wasika ke tashe. Sannan ki samu turare mai kamshi ki fesa, sai ki sa a ambulan sai ki aje masa a inda kika san ba mai gani sai shi, misali cikin aljihun kayan da zai sa zuwa Sallar idi, ko cikin battarsa ta saka kudi (wallet). Maigida, kana iya shirya wasu kayatattun kalamai masu dadi na nuna so da kauna, sai ka kai a tsara su kuma a kawata su da furanni da kaloli masu kyau, sai a buga a yananyin katin  gaisuwa (greeting cards), ko wanda za a sa a gilashin saka hotuna (photo frame), ko a yi shi kamar irin yadda akan yi kalanda da sauransu. Lokacin da uwargida ta ci adon kwalliyar sallarta, sai a maigida ya ba ta wannan taswirar kauna.
5.      Sadaukarwa: Maigida ya hakura da duk wani yawon sada zumunci ga ‘yan uwa da abokai, ya kyautar da yinin ranar sallah gaba daya ga iyalansa don sadar da kauna da sabunta soyayya. Misali, kamar ya taya uwargidanshi aikin safiyar sallah; ta yi wa yara wanka da shiryasu, soye-soye da tarbar bakin sallah, da sauran ayyukan gida da ya ga sun dace ya taimaka, wannan shi ne soyayya dumammiya mai dumamawa, ba maigida ya yi kwance ya bar uwargida da aiki ita kadai ba.
Da fatan Allah Ya sa a yi shagalin Sallah a kare lafiya, amin. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.