✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sharri kayan kwalba

Bisa ga dukkan alamu za a dade ba a mance da gagarumin taron da tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Bahari ya yi a ranar Juma’ar…

Bisa ga dukkan alamu za a dade ba a mance da gagarumin taron da tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Bahari ya yi a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja ba don kaddamar da burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a karo na hudu. Babu shakka taro ya yi taro, talakawan da suka ci goron gayyata sun wanwanke kafafunsu, suka bibbiya kudin sufuri daga garuruwansu zuwa Abuja daga aljiffansu, don nuna tsabagen kauna da goyon baya ga gwarzonsu. Wannan ne ya sa shugabannin jam’iyyar PDP kidimewa, idanunsu suka yi jawur, hankulansu kuma suka dugunzuma domin sun san kwanan zancen, suna tsoron faduwar bakar tasa a gaban Janar Buhari.

Saboda ganin cewa tafukan hannuwansu ba za su iya kakkare hasken ranar da ta fito ba, sai shugabannin jam’iyyar PDP, tare da kungiyar fafutikar fitar da Shugaba Goodluck don tsayawa takarar 2015, TAN suka dauki matakin shafa wa jam’iyyar APC da kuma manyan jami’anta kashin kaji, haka nan ba gairan balle dan dalili don dai kawai a bakanta su a idanun ‘yan Najeriya.
A lokacin da aka yi wancan taro na Buhari a Abuja, Cif Audu Ogbe, daya daga cikin jiga-jigan jagororin jam’iyyar APC, ya nanata abin da ke damun daukacin al’ummomin Najeriya dangane da sakacin Gwamnatin Jonathan na rashin daukar matakan da suka dace kan kari don kubutar da ‘yan matan makarantar Chibo da aka yi awon gaba da su, aka jefa su cikin bakar ukuba, fiye da watanni shida da suka shude, ba amo, ba labari.
Cif Audu Ogbe ya yaba da kwazo da kuma jajircewar da wata kungiya mai gwagwarmayar ganin an dawo da wadancan ‘yan mata, watau #Bring Back Our Girls, wacce ‘ya’yanta da shugabanninta suka yi sansani a Abuja don tabbatar da haka fiye da watanni hudu da suka gabata, ya kuma nuna cewa yawancin shugabannin waccan kungiyar duk ‘ya’yan jam’iyyar APC ne.
Haka nan kuma an gabatar da Hajiya Khadija Bala Usman a lokacin da za ta yi jawabi a wajen taron Buhari a matsayin daya daga cikin shugabannin matan jam’iyyar APC, sai al’amarin ya zama abin magana ga jam’iyyar PDP da makararrabanta. Saboda ba su da wani aikin yi, ba su kuma da abin da za su yi amfani da shi don kushe wancan gagarumin taron na Buhari a Abuja, sai suka kitsa wata kutungwila da wadancan abubuwa guda biyu don tayar da wata sabuwar husumar da suke gani za ta iya karya laggon jam’iyyar APC da kuma mabiya Janar Muhammadu Buhari.
Cikin dan kankanen lokaci sai ga shi nan suna ta kashe makudan kudin da ba su jin zafinsu, domin ba su san asalinsu ba, wajen yin tallace-tallace a gidajen talbijin suna nuna yadda Cif Audu Ogbe ke kwanzarta kokarin waccan kungiyar matan masu gwagwagwa da gwamnati don a sako wadancan ‘yan matan, wadanda kuma ya ce shugabanninsu ‘yan jam’iyyar APC ne, cikinsu kuwa har da Hajiya Khadiza Bala Usman a matsayin daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar gwagwarmayar matan. Manufarsu a nan, kamar yadda suka fayyace, shi ne tozarta take-taken shugabannin jam’iyyar APC, wadanda PDP ta kira marasa imani da tausayi domin kuwa sun mayar da bala’in da ya gallabi iyayen yara da sauran jama’ar Najeriya, batun siyasa don tsabar rashin sanin ya kamata da niyyar bata gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.
To, amma bisa ga dukkan alamu shugabannin jam’iyyar PDP da wadanda suka tsiri wannan al’amari na bata shugabannin APC da kuma na kungiyar matan da ke gwagwarmaya don a sako wadancan ‘yan matan makaranta, sun yi wa kawunansu ne, domin kuwa fitsarin fako ne suka yi, zai kuma yi tartsatsi a jikinsu. Ai da ma shi sharri kayan kwalba ne, idan mai dauke da shi ya kifar za su farfashe, sa’annan kuma ya taka abinsa.
Duniya gaba daya na sane da matsalar wadancan ’yan mata da kuma wadanda ke da hakkin ganin an sako su. Suna kuma sane da irin damuwar da daukacin jama’ar kasar nan suka nuna saboda halin adankiyan (ko’in kula) da gwamnati Shugaba Jonathan ke nunawa game da su, da kuma yadda ta fi mayar da hankalinta wajen ayyukan assha da sharholiya sa’ilin da iyayen yaran nan ke kwana, suna tashi cikin tsananin bakin ciki da takaici.
Abin da dai jam’iyyar PDP da manyan jami’anta dai ke gudu sai ya faru idan ba ta mayar da hankalinta ba gadan-gadan wajen ceto wadancan ‘yan mata kafin zuwan zaben 2015. Rashin saduwarsu da iyayensu zai iya haddasa janyo faduwar jam’iyyar PDP warwas, kuma ana jin cewa kafin a kai ga haka jam’iyyar na iya haddasa matsalolin da za su tayar da zaune-tsaye a kasar, kamar yadda take yi a dukkan lokutan da ta fahimci cewa jama’a sun dawo daga rakiyarta kuma ’yan adawa na samun galba a kanta. Sau da yawa takan haddasa yamutsi da tarzoma a wasu wurare idan ta ga ba za ta samu galbar zabe ba, sa’annan ta dora laifin haka kan jam’iyyar adawa da shugabanninta.
Ko kungiyar matan da ake gwagwarmayar komowar ‘yan matan makarantar Chibok na da alaka da jam’iyyar APC, ko kuma ba haka ba ne, wajibi ne jama’ar kasar nan, ciki kuwa har da ‘yan jam’iyyar APC su ci gaba da yin korafi saboda gazawar gwamnatin Shugaba Jonathan wajen ceto su. A sabili da batun kokarin Buhari na sake tsayawa takara ne cikinsu ya duri ruwa, wasu na ta zawo kamar farar kura, har hakan ya sa suka kago wata sabuwar dabarar rudar talakawan Najeriya da batun tsagaita wutar yaki da kungiyar Boko Haram da kuma shafa masu mai a baka game da sako wadancan ‘yan matan. Oho dai, wanda duk ya daure kura shi zai kwance ta.