✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaye-shaye Ke Rura Matsalar Tsaro A Yobe —Sarkin Fika

Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun kwayoyi a matsayin abin da ke…

Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun kwayoyi a matsayin abin da ke rura wutar rashin tsaro a jihar.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin wata liyafa da ya shirya ga ’yan jarida a fadarsa da ke Karamar Hukumar Potiskum.

Ya ce harin baya-bayan nan da aka kai a yankin Gurjaje da ke Karamar Hukumar Fika ta jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya tare da lalata gidaje sama da 100, ya tabbatar masa da alakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da rashin tsaro.

Sarkin Fika ya bukaci gwamnatin jihar da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta fito da tsare-tsaren da za su dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da cigaba a yankunan da lamarin ya shafa, yana mai kokawa kan tabarbarewar tattalin arziki a kasar.