✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekaru 14 bayan rasuwar Alhaji Garba Bichi

Yau shekara 14 da Alhaji Garba Ali bichi ya koma ga MahaliccinSa. Wannan gwarzon al’umma ya shahara a harkokin kasuwanci a fadin Afirka ta Yamma.…

Marigayi Alhaji Garba Ali BichiYau shekara 14 da Alhaji Garba Ali bichi ya koma ga MahaliccinSa. Wannan gwarzon al’umma ya shahara a harkokin kasuwanci a fadin Afirka ta Yamma. Don haka muke tunawa da irin gudunmuwar ya bai wa al’umma da kasarsa ta haihuwa a tsawon rayuwarsa. Rayuwar Garban Bichi abin koyi ce ga wannan al’umma don samun mafita daga matsalolin da suka dabaibaye al’umma a zamantakewa da harkokin tattalin arziki.
Mika wuya ga Allah (SWT) shi ne jigo sakon Annabawa da aka aiko ga al’ummomi, don haka suka shafe zamaninsu suna masu wa’azi. Bisa wannan dalilin ake so Musulmi ya yi imani da kaddara ta sharri ko ta alkhairi, duk da cewa an bai wa dan Adam kaifin basirar yin zabi tsakanin abu mai kyau da mara kyau. Musulmin da ya samu albarkar rayuwa ba a son yi masa takaicin mutuwa, illa dai a dauka jarrabawa ce daga Mahaliccinsa, wanda Ke da karfin iko a kan kowa da komai.
Alkur’ani mai girma ya bayyana cewa: “Allah (SWT) mai girma da dauka ya halicci mutua da rayuwa don ya jarraba ku, don a tantance kowane ne a tsakanin zai kasance mai kyakkyawar dabi’a,” don haka kankan da kai ita ce mafita, ta hanyar mika wuya ga Allah (SWT), Mahaliccin duniya da lahira.
Rasuwar Alhaji Garba Ali Bichi, ba wani al’amari ba ne da za a kale shi ta wata fuska mabambanciya daga ikon Allah, Wanda ya fi kowa sanin mafi alkhairi dacewar lokacin da ya dace ya dauki rayuwar bawanSa. Tunda Allah ne ke da halittunSa, to babu bambanci a wurin Allah idan ya dauki ran dan shekara 10 ko 20 ko 30 ko 100 wanda ya zauni duniya.
Alhaji Garba Ali Bichi ya amsa kiran Mahaliccinsa, Allah Madaukakin Sarki, a ranar Juma’a, 24 ga Satumbar 1999, bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya a gidansa da ke karamar Hukumar Bichi, a Jihar Kano. Ya bar gadon arziki ga masu tasowa, ba wai ga ’ya’yansa da ’yan uwa da al’ummar garinsu kawai ba.
Alhaji Garba Ali Bichi ya kasance daya daga cikin fitattun ’ya’yan Yankin Arewa. Marigayin ya kasance a cikin jerin wadanda suka amsa kiran Firimiyan Jihar Arewa, Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, wanda ya jagoranci wannan yankin a tsakanin shekarun 1960 zuwa 1966. Kuma a zamaninsa an samu ci gaba da bunkasar harkokin noma, ba ma a Najeriya ba, har da sauran yanbmunan Afirka ta yammma.
Alhaji Garba Bichi bai takaita gudunmuwarsa wajen bunkasa noma ba, har da harkokin kasuwanci da masana’antu, inda ya fara harkokin kasuwanci da sule 70, har ya kai ga matsayin mai kafa masana’antu a yankin Afirka ta Yamma.
Marigayi ya yi matukar hangen nesa da kwazo har ya kai ga shiga cikin jerin hamshakan masu kudi a garinsu, wato karamar Hukumar Bichi da daukacin kasar Hausa. Baya ga abin da aka sanshi da shi na kasuwanci, shi mutum ne da ya yi kokarin wajen bunkasa ilimin addini da na zamani, don ya shigar da kansa ajin yaki da jahilci bayan ya kware a akratun Alkur’ani A wajen malaminsa, wanda ya koya masa yadda ake karatun Alkur’ani a mahaifarsa da ke Haggalawa a garin Bichi.
daukakar da ya samu a cikin al’umma ba ta rufe masa ido ba, don haka ya sanya daukacin ’ya’yansa makarantar Firamare ta Haggalawa, don su samu damar cudanya da mutane, wadanda suke ganin iyayensu bas u da amtsayi irin nasa a cikin al’umma.
Idan aka yi nazarin tarihin rayuwar Marigayi Alhaji Garba Bichi, za a fahimci ya rasu daidai lokacin da masu tasowa ke bukatar tarbiyya a fannoni na rayuwa daga mutane masu gogewa irinsa.
Lokacin da aka bayar da sanarwar rasuwar Garba Bichi, wannan yanki ya shiga cikin dimuwa, musamman in an yi la’akari da irin gudunmuwar da ya bayar wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya, bisa tafarkin tsarin kare muradun Arewa, wanda Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya bullo da shi.
Musulmi da dama a duniya sun yi makokin rasuwarsa, musammman in an yi la’akari da gudunmuwar da ya bayar wajen bunkasa makarantun Islamiyya da Masalaltai, da taimaka wa marasa galihu a kowace rana, don yaki da fatara da talauci a cikin al’ummmar da yake zaune.
Za a rika tunawa da Alhaji Garba Bichi kan irin tarbiyyar da ya bai wa ’ya’yansa da ’ya’yan makwafta, musamman ma idan aka yi la’akari da cewa daukacin ’ya’yansa duk sun samu horo a fannonin ilimi, wanda ya hada da na addini da na zamani, inda wasu suka tsunduma cikin harkokin kasuwanci da siyasa da ayyukan gwamnati. ’Ya’yansa sun yi fice, inda daya daga cikinsu Alhaji Ahmad Garba Bichi ya yi ministan harkokin kasuwa, ya kuma yi iya kokarinsa wajen koyi da mahaifinsa, don yin hidima ga al’umma.
Rayuwar marigayi Alhaji Garba Bichi abin koyi ne ga wadanda ke kokarin ganin Najeriya ta samu amfita, ta kuma ci gaba a daukacin al’amura da aka sa a gaba. Mun yi amfani da wannan rubutu ne don isar da ta’aziyyarmu, ba wai ga ’ya’yansa da ’yan uwa kawai ba, a’a, har ma da daukacin duniyar Musulmi.
Muna fatan Alah Ya yi masa rahama, Ya gafarta wa Alhaji Garba Bichi, wanda ya amsa kiran Mahaliccinsa a watan Jumadal-Akhir na Hijiriyyar 1420, wanda ya yi daidai da ranar 24 ga Satumbar 1999 Miladiyyar Masihiyya. Allah Ya amsa addu’armu, ya kuma yi mana kariya daga illolin shaidan, sannan ya wadata kasar mu da zaman lafiya.

Za a iya samun Aliyu Umar a 08065570493