✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirye-shiryen aikin Hajjin bana ya kankama a Filato

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato, Barista Auwal Abdullahi ya ce zuwa yanzu, shirye-shiryen aikin Hajjin bana sun kankama a jihar.  Sakataren…

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato, Barista Auwal Abdullahi ya ce zuwa yanzu, shirye-shiryen aikin Hajjin bana sun kankama a jihar. 

Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos, inda ya ce a bana an bai wa jihar kujerun aikin Hajji 1111, kuma zuwa yanzu majiyyata suna ta biyan kudeden aikin Hajjin.

Sakataren ya ce tun a watan Janairun bana ne ma’aikatan hukumar suka tafi kasa Mai tsarki, suka kama wa alhazan jihar masaukai. “Bayan da aka ba mu jagorancin wannan hukuma, mun tafi kasa Mai tsarki mun gane wa idanunmu wadannan masaukai da aka kama wa maniyyatan Jihar Filato, kuma mun gamsu da ingancin masaukan. Kuma in Allah Ya yardar a gobe, za mu sake komawa kasa Mai tsarki, don ganin mun tsara dukan abubuwa da za su taimaka wa alhazan Jihar Filato wajen gudanar aikin Hajjin bana cikin jin dadi da kwanciyar hankali,” inji Babban Sakataren.

Ya ce a bana hukumar za ta dauki zakakuran ma’aikata da za su aiki ba dare ba rana wajen taimaka wa alhazan Jihar Filato, sai ya y kira ga maniyyatan jihar su zo su biya kudaden kujerunsu, wadanda kuma suka fara ajiye kudadensu, su zo su cika su. Domin a karshen wannan wata ne za a kammala karbar kudaden, kamar yadda Hukumar Hajji ta kasa ta sanar.