✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba al-Bashir zai kara tsayawa takara

Shugaban kasar Sudan Umar al-Bashir zai kara tsayawa takara a zaben da za a gudanar a kasar a badi, duk da cewa a baya ya…

Shugaban kasar Sudan Umar al-Bashir zai kara tsayawa takara a zaben da za a gudanar a kasar a badi, duk da cewa a baya ya ce zai yar da kwallon mangwaro bayan ya kwashe shekara 25 akan mulki.

Kamar yadda wani na kusa da shugaban ya bayyana cewa shugaban na kan gaba da sauran ’yan takara hudu bayan wata matsaya da jam’iyya mai mulki ta NCP ta cin ma.
Idan dai ba a manta ba Kotun Manyan Laifuka ta Duniya da ke birnin Hague ta ba da sammacin kama shugaban bisa zargin cewa yana da hannu a rikicin yankin Darfur. Zargin da shugaban yake musantawa. Har ila yau, kungiyar Tarayyar Afirka goyi bayan Mista Bashir. Inda ta ce shugaban da ke kan mulki ba zai iya bayyana a gaban kotun ba saboda kariyar da shuganni ke da ita. Hakazalika, Sudan na daga cikin kasashen da basu amince da kotun ba.
Kodayake, wadanda suke adawa da shi suna bayyana shi da cewa yana daya cikin shugabanni a nahiyar Afirka da ke mulkin kama karya.Shugaban mai shekara 70, ya karbe mulki ne bayan da ya yi juyin mulki a shekarar 1989, kuma ya lashe zabuka uku tun bayan darewarsa karagar mulki.
Kodayake, a shekarar 2011, wani jami’i a jam’iyyar NCP ya ba da tabbacin cewa Mista al-Bashir ba zai tsaya a zaben shekarar 2015. Sai dai tun a wanacan lokacin ’yan adawa da masu sharhi kan al’amura a kasar suka sa shakku, inda suka ce an fadi hakan ne domin a tsoron kada guguwar sauyin da ta faru a kasashen Larabawa ta karasa kasar.