✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban jam’iyyar APC da ya bata ya kai kansa wurin ’yan sanda

Rundunar ’yan sadan jihar Kaduna sun bayyana cewa Danladi Wada, shugaban bangaren hamayya na jam’iyyar APC a Kaduna wanda jam’iyyar ta shelanta cewa ya bata,…

Rundunar ’yan sadan jihar Kaduna sun bayyana cewa Danladi Wada, shugaban bangaren hamayya na jam’iyyar APC a Kaduna wanda jam’iyyar ta shelanta cewa ya bata, ya kai kansa ofishin ’yan sandan jihar.
 
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Autin Iwar ya tabbatar da aukuwar hakan a sakon wayar da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata.
 
“Haka ne ya kai kansa wurin ’yan sanda kuma muna bincike a kan lamarin”. Inji shi.
 
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa mai magana da yawun bangaren adawar na jam’iyyar APC, Murtala Abubakar ya ce suna sa rana Wada ya kai rahoto ofishin ’yan sandan jihar don ya bayar da bayanai bayan da wadanda suka sace shi suka sako shi.
 
Abubakar ya ce an saki shugaban bangaren hamaiyar na jam’iyyar a ranar Lahadi a garin Zariya.