✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Majalisa ya nemi mambobin APC su jingine batun neman mukamai sai…

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya nemi jagorori da mambobin jam’iyyun da suka narke a sabuwar Jam’iyyar APC su yi hakuri…

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya nemi jagorori da mambobin jam’iyyun da suka narke a sabuwar Jam’iyyar APC su yi hakuri da batun neman mukamai da suke yi har zuwa lokacin da za a kammala dukan shirye-shiryen kasa mukaman kamar yadda yake a ka’idar hadewarsu.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai dangane da yadda wasu ke zakewa suna kiran kansu shugabannin sabuwar jam’iyyar, inda ya ce masu wannan buri na neman matsayi a cikin sabuwar jam’iyyar su yi hakuri kada su kawo nakasu a sabuwar tafiya da aka fara don samun damar karbe mulki daga hannun Jam’iyyar PDP wadda ta dauki sama da shekara 14 tana gasa wa al’umma aya a hannu.
Ya ce masu cewa ana ba da kudin gudanar da ayyukan raya mazabu kai-tsaye ga ’yan majalisu su sani ba aikin ’yan majalisa ne a ba su kudin gudanar da ayyukan raya mazabunsu ba, hakkin haka na wuyan majalisar zartarwa ne, su aikinsu shi ne yin dokoki da ba da shawarar wuraren da ke bukatar a gudanar musu da ayyukan raya kasa a mazabunsu don neman sahalewar majalisar zartaswa.