✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Majalisar Dattawa ya nada mataimaka

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya nada mataimaka biyu da za su yi aiki da shi suka hada da Alhaji Muhammad Aji, Shugaban Ma’aikata…

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya nada mataimaka biyu da za su yi aiki da shi suka hada da Alhaji Muhammad Aji, Shugaban Ma’aikata da kuma Mista Festus Adedayo, Mai taimaka masa a harkar watsa labarai.

Sanarwar da ta fito daga Mai taimaka wa Shugaban Majalisar a kan sha’anin mulki Mista Betty Okoroh, ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.

Ta ce nadin an yi shi ne bisa cancanta da lura gogewa tare da bibiyar nasarorin da jami’an biyu suka samu a baya.

Shugaban Majalisar ce ya bukaci ya yi aiki da su domin su taimaka masa wajen sauke nauyin da yake kansa na shugabancin majalisar kamar yadda takardar ta kunsa.

Kafin nadin Alhaji Aji, yana  rike da mukamin shugaban sashin gudanarwa a  Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), kuma yana da digiri na biyu a kan   ilimi da shugabanci daga Jami’ar Maiduguri. Aji ya fara aiki a Jami’ar Maiduguri a 1987 a matsayin mai taimakawa kan sha’anin mulki kafin ya zama Magatakarda jami’ar a 1997. Kuma ya yi aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri inda ya rike mukamin Babban Darakta a shekarar 2016.

Shi kuwa Mista Adedayo yana da digiri na uku a fannin aikin jarida daga Jami’ar Ibadan kuma yana daya daga cikin editocin jaridar Tribune.

Ya taba zama Mataimaki na Musamman kan Watsa labarai ga Gwamnan Jihar Oyo a shekarar 2011 zuwa 2015, kuma  ya rike irin wannan matsayi na mai ba da shawara ga tsohon Gwamnan Jihar Enugu a shekarar 2003 zuwa 2004.