✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabanni da jami’an difulomasiya ba su gamsu da jawabin Suu Kyi ba

Shugabar Myanmar  Aung San Suu Kyi na fuskiantar matsin lamba daga hukumomin duniya kan yadda ta tarairayi rikicin ‘’yan gudun hijirar rohingya da suka fito…

Shugabar Myanmar  Aung San Suu Kyi na fuskiantar matsin lamba daga hukumomin duniya kan yadda ta tarairayi rikicin ‘’yan gudun hijirar rohingya da suka fito daga  Jihar Rakhine.

A jawabinta na ranar Talatar da ta gabatar shugabar farar hula ta kasar Aung San Suu Kyi ta soki lamirin yadda aka keta haddin dan adam, amma ba ta zargin sojojin kasar ko ta kawo yadda za a shawo kan kisan kare dangi da aka yi wa Musulmin kasar ba.

Shugabanin kasashe da jami’an difulomasiya daga kasashe da dama tuni suka nuna takaicinsu kan matsayin da ta dauka. Domin a halin yanzu akwai fiye da ‘’Yan rohingya dubu 400 da suka yi hijira zuwa Bangladesh tun cikin Agustan bana.

Mummunan bala’i da ya auka wa Rakhine a kwanakin nan shi ne farmakin da ake kai wa ofisoshin ’yan sanda da ke fadin jihar tun a karshen watan da ya gabata, wanda aka dora alhakinsa kan gungun ’yan tawaye na kungiyar sojojin Arakan Rohingya.

An halaka dimbin mutane lokacin da sojoji suka kai farmaki, kuma ana zargin  an kone kauyuka da dama, tare da tursasa Rohingya su fice daga wuraren.

A jawabin farko da ta gabatar kan rikicin da ya barke, Ms Suu Kyi t ace: 

• Babu karon battar da aka yi  a Jihar Arewacin kasar tun baya ga na ranar 5 ga Satumba

• Mafi yawan Musulmi sun yarda su tsaya, don haka wannan ya nuna lamarin bai yi muni ba.

• Gwamnati ta yi kokari a ’yan shekarun baya-bayan nan don kyautata halin rayuwar daukacin mutanen Rakhine da suka hada da Musulmi

• Kuma za a kyale daukacin ’yan gudun hijira su koma gida bayan an tantance su.

Mutumin da ya fi sukar lamirin yadda gwamnatin Myammar ta tun kari lamarin shi ne shugaban kasar Turkiyya, Racep Eerdogan. Majalisar dinkin Duniya ta bukaci a yi wa Musulmin Raohingya adalci, ta yadda doka za ta tabbatar da matsayinsu na ’yan kasa a Myanmar.