✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabar Mata ta APC a Jihar Kebbi ta nemi kira a zauna lafiya

Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi Hajiya Tsahara Bawa ta nanata muhinmancin zaman lafiya da kuma karbar katin rijistar zabe. Hajiya Tsahara Bawa…

Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi Hajiya Tsahara Bawa ta nanata muhinmancin zaman lafiya da kuma karbar katin rijistar zabe. Hajiya Tsahara Bawa ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu a ofishinta da ke sakatariyar Jam’iyyar APC da ke Birnin Kebbi.

Shugabar Matan ta ce duk da jam’iyyarsu ta APC ta samu karbuwa a fadin kasar nan abu ne mai muhinmancin gaske yadda ’ya’yan jam’iyyar su ci gaba da zaman lafiya domin cimma burinsu na cinye zabe mai zuwa.
Ta ce wajibi ne shugabannin APC su ci gaba da lalubo tare da bin duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da zaman lafiya domin suke da nasara in Allah Ya yarda domin cinye zabubbukan da za a gudanar a watan nan na Maris, kuma hakan ba zai samu ba sai da hadin kan ’ya’yan Jam’iyyar APC baki daya.
Da take magana game da shirin karbar katin zaben ta bukaci daukacin matan Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi da ba su karbi rijistarsu ba da su je su karba domin su zabi wadanda suke so.