✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasa: An bar malaman Musulunci a baya —Sheikh Ibrahim Khalil

Abin da bai dace ba shi ne malami ya fito baro-baro yana bayyana goyon baya.

A daidai lokacin da ya rage saura makonni kadan a gudanar da zabubbukan bana, har yanzu ana musayar yawu a kan dacewar shigar malaman Musulunci cikin harkokin siyasa.

Wasu da dama suna tunanin bai kamata malamai su tsoma bakinsu a harkokin siyasa ba, ballantana su tsaya takara.

A wani gefen kuma, wasu na ganin akwai bukatar malamai da dama su shiga a dama da su a harkokin siyasar, musamman ganin yadda malaman addinin Kirista suka yi nisa a lamarin, inda da yawansu suke tsayawa takara, wasu kuma suke karbar manyan mukamai.

Aminiya ta ruwaito a muhawarar makon jiya, yadda mutane suke kallon shigar malaman na Musulunci siyasa, inda wasu suke na’am, wasu kuma suke cewa bai kamata ba.

Wannan ya sa Aminiya ta tattaunawa da Sheikh Ibrahim Khalil, wanda yake takarar Gwamnan Jihar Kano da kuma Farfesa Ibrahim Makari daya daga cikin limaman Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, wanda bai cika son shigar malamai harkar siyasa ba.

Game da yadda yake kallon lamarin, Sheikh Khaleel ya ce, “ Ita siyasa kalma ce ta Larabci, ma’anarta jibintar lamarin jama’a da jagorantarsu da kuma nuna musu hanya.

Har ila yau, ita siyasa da ake gani kashi uku ce. Na farko akwai siyasa ta wayar da kan mutane yadda za su san amfaninta ga al’umma da alherinta da kuma muhimmancin yadda mutane za su san wanda ya kamata su zaba da kuma yadda za su ci moriyarta.

Na biyu shi ne wadanda za su fito su nuna wa mutane irin mutane da ya kamata su zaba. Su gaya wa mutane sunansa su ayyana su, idan ba su yi abin da ya kamata ba, su canja su tare da malaman nan ba wani bangare suke dauka ba.

Na uku shi ne shiga takara. Duk da cewa a nan ba za a ce kowa ya zo ya yi takara ba, saboda dabi’a ta mulki da kuma magana ta kudi da sauransu, kasancaewar ba kowa zai kubuta daga hadarin kudi ko mulki ba.

Haka kuma sauran abubuwan gazawa da ke kansu ba za su sa a ce dukkan malamai su zo su shiga siyasa ba.

Haka kuma saboda ma kada a tare a wuri daya shi ma ba zai sa a ce dukkan malaman su shiga siyasa ba, dole wasu su tsaya a wasu abubuwan rayuwa.

Akwai batun raba-kafa don kada ya zama ka san dukkan kwanka a kwando daya. Wannan shi ya sa muke ta kiran malamai kowa ya tsaya a ajin da ya kamace shi.”

An bar malaman Musulunci a baya a siyasa

Sheikh Ibrahim Khalil ya ce, “Ko shakka babu an bar malaman Musulunci a baya a fagen siyasa. Domin za a iya cewa barin da aka yi musu a baya ya kai kamar nisan sama da kasa.

An bar su a baya a siyasar tatatlin arziki da siyasar mulki da siyasar rayuwa.

Wasu an bar su a baya ne saboda gwamnatoci kamar a kasashen Larabawa da kuma Afirka kai har da Najeriya, ba su san me ke faruwa ba.

Haka kuma an bar su a baya saboda yadda suka fahimci addinin, ma’ana sun fahimce shi a kuntace kuma saboda ba su fahimci inda rayuwa ta sa gaba ba.

Abin da ya sa malamai ke tsoron shiga siyasa

Ya ce, abin da ke sa malamai tsoron shiga siyasa, “Na farko shi ne rashin fahimtar rayuwa. Na biyu kuma shi ne yadda suke ganin ’yan siyasa na gudanar da rayuwa da mu’amalarsu, musamman ganin yadda suke sa a ci mutuncin mutane da sauransu.

Da kuma ganin yadda mutane idonsu ya rufe da son abin duniya, do haka suna tsoron kada su je su ma su shiga cikin wannan.

Haka idan aka duba ’yan siyasa mutane ne masu son kai, za su iya yin komai don ganin sun samu biyan bukata, ko da hakan na nufin za su kawar da mutum daga bayan kasa.

Wadannan da makamantansu ne ke sa malamai jin tsoron shiga siyasa. Idan aka dauki kamar ni mutane da dama na tambaya ta me ya sa ka shiga siyasa bayan ga irin cakwakiyar da ke cikinta.

Magana a mumbari kadai ba zai wadatar ba

Malam Ibrahim ya ce, “A gaskiya magana a mumbari ba zai wadatar ba, domin a wasu lokuta su kansu malaman sukan yi kuskure kuma wa’azi kadai bai taba canza rayuwar dan Adam ba a duk duniya.

Shi wa’azi yana wayar wa mutum kai ne sai dai ba za a rasa ’yan wasu abubuwa da mutum zai dauka a ciki ba.

Amma muhimmin abin da mutum yake yi, wa’azi bai fiye canza shi ba. Kuma a wasu lokuta akan yi amfani da malamai su hau mumbari su yi abin da bai dace ba.

Misali a lokacin zaben shekarar 2015 malamai sun hau munbari suka Musuluntar da wata jam’iyya tare da kafirta wata jam’iyyar.

Shi mumbari ba abin da zai canza na rayuwar al’umma. Sai dai idan malamai sun shiga siyasar kanta. Idan kika dauki wa’azi ko a rediyo ko a mumbari sai wanda ya ga dama ne zai saurara, amma shi mulki yana tasiri a rayuwar al’umma don zai taba mutum ko ta hanyar dadi ko akasinsa.

Misali idan ka dauki wani bayani da Dokta Muhajir na Malesiya ya yi cewa, amfanin da al’umma duk suka samu daga gare shi a matsayin da yake rike da mulki ya fi na wanda suka samu a matsayinsa na likita.

Ya ce, idan da zai yi nadama to sai dai ya yi nadama na zamowarsa likita a kan zamowarsa shugaba.

Wani misalin kuma shi ne idan aka dauki sinima din Paris da ke Kano kowa ya san abin da ake yi.

Malamai sun yi iya kokarinsu wajen yin wa’azi da nusar da jama’a kan guje wa abin da ake yi, amma Paris ba ta canza ba har sai da Alalh Ya kawo Sabo Bakin Zuwo a matsayin Gwamnan Jihar Kano, inda a cikin kankanin lokaci ya mayar da wurin ya zama asibitin haihuwa kuma tun daga wancan lokacin abubuwa suka canza.

Kin ga a nan mulki ne ya yi tasiri ba wa’azi ba.

Kira ga malamai

Sheikh Ibrahim Khaleel ya ce, “Abu na farko shi ne su san martaba da darajar da Allah Ya yi musu. Ya kamata su cire kwadayi daga ransu.

Ya kamata su fahimci yadda rayuwa ta sa gaba. Da yadda siyasar duniya ta sa gaba. Kuma su yi kokari su samu abin dogaro da kai.”

Ba kowace irin siyasa malamai za su yi ba —Farfesa Makari

Daya daga cikin limaman Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya ce, ba laifi ba ne malaman Musulunci su shiga lamarin siyasa ko kusantar ma’abota mulki matukar za su tsare ka’ida a lamarin.

Farfesa Ibrahim Makari wanda ya bayyana haka a yayin zantawa da Aminiya, inda ya ce, “Idan mai mulki yana kamanta hali irin na su Sayyidina Umar ko Sayyidina Ali (Allah Ya kara musu yarda), to ai irin su ya cancanta a kusance su da nagarta.

Sabanin masu mulki wadanda kusantar su sai dai ya zubar da kima a fuskar addini ko sauran al’amuran yau da kullum.”

Shehin Malamin ya ce, wajibi ne malamai su kasance a matsayin fitila mai haskaka wa al’umma a kan sha’anin jagoranci da samar da jagorori na gari, ta hanyar bayyana siffofin wanda ya kamata a zaba tare da sanar da jama’a hakkokinsu da kuma su kansu jagororin.

“Abin da bai dace ba shi ne malami ya fito baro-baro yana bayyana goyon baya tare da yi wa wani dan siyasa kamfe a kan sauran abokan karawarsa, watakila ma yana kan mumbarin masallaci ko dandalin wa’azi ko kuma ya rika bin su wajen kamfe.

To wannan kam tamkar ya ci amanar da aka damka masa ce kuma zai iya kaiwa ga zubar da kimarsa da shi kansa addinin a wajen jama’a,” in ji shi.

Sheikh Makari ya ce, takaita goyon bayan malami na zahiri ga wata jam’iyya ko dan takara guda, na iya mayar da Musulmi ko addininsu saniyar ware idan aka samu akasi wajen samun nasara a zabe.

Ya ce, “Ya kamata a san cewa dukkan jam’iyyun kasar nan tsare-tsarensu sun ta’allaka ne kawai a kan kasa, ba lamarin addini a ciki, sannan babbar bukatarsu ita ce yadda za su kai ga nasara.”

Sheikh Makari ya ce, za a iya samun na gari ko akasin hakan a dukkan lamura da suka hada da jagororin muki da na siyasa da kuma addini, inda ya bukaci masu zabe su tabbata sun yi zabe kan nagarta da kuma cancanta.