✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasar Kano

Assalamu alaikum, barkarmu da wannan lokaci tare da fatan dukan muna cikin koshin lafiya, yaya aka ji da aiki? Yau zan mai da hankali ne…

Assalamu alaikum, barkarmu da wannan lokaci tare da fatan dukan muna cikin koshin lafiya, yaya aka ji da aiki?

Yau zan mai da hankali ne kacokan a kan siyasar jiha mafi yawan jama’a, wato jihar marigayi Malam Aminu Wato Kano ke nan. Tabbas Jihar Kano jiha ce wadda Allah Madaukakin Sarki ya arzuta ta da mutane masu hazaka da basira da kwazo da sanin ya kamata, sannan Kanawa mutane ne, masu kawaici da nuna da’a da dattako.

Tun farkon samuwar wannan kasa tamu Najeriya, Jihar Kano sananniya ce wajen kokarinta na kawo dukan ci gaban da za a yi alfahari da ita, wanda a cikin jajircewarta ce ta sa Arewa ta yi fice kuma ta samu daukaka da kima da daraja a idon duniya. Kamar dai yadda masu salon iya zance suke fada cewa ‘Kano ta Dabo Tumbin Giwa, Yaro ko da me ka zo an fi ka,” ko shakka babu wannan haka yake.

Tun kafin zuwan siyasa Turawan mulkin mallaka sun samu Kano zaune da mutanenta lafiya lau, sannan ko da siyasar ta isko mutanen Jihar Kano suna da kyakyawar mu’amala da juna a tsakaninsu, suna taimakekeniya da junansu, suna son junansu, hasali ma ma, wanda ba a Kano yake ba, ba zai gane sirrin mutanen Kano ba, dalili kuwa shi ne, sun zama tamkar ’yan uwan juna.

Babu ko shakka, sagegeduwar siyasar wannan zamani tana kokarin ruguza Jihar Kano da mutanenta, lura da yadda siyasa ta shiga cikin al’ummar jihar take kokarin daukar wani sabon salo, wanda babu inda zai kai jihar sai tabarbarewa, Allah Ya kyauta ba ma fatar haka ya kasance, domin Jihar Kano ita ce Arewa. Ko shakka babu, irin abin da yake faruwa a yanzu a Jihar Kano saboda siyasa, abin tir da Allah wadai ne, kuma abu ne wanda duk wani dan Arewa mai son ci gaban Arewa dan kishin al’ummar Arewa, zai yi bakin ciki da shi matuka ainun.

Da ma wadansu makiya Arewa hadi da wadansu daga cikin gurbatattun al’ummar Arewa sun kasa lalubo hanyoyin da za su yi amfani da su wajen wargaza Jihar Kano, shi ne suka fake da siyasa suke cin karensu ba babbaka. Hakika wadansu daga cikin matasan Jihar Kano sun ba mu kunya kuma sun ba mu mamaki, irin yadda wadansu tsirarun mutane suka hada kai da su, suka ba su dan abin da bai taka kara ya karya ba domin su ta da husuma su illata da raunata ’yan uwansu na jini, wadanda suke da matukar amfani gare su.

Ko shakka babu, irin abin da ake zargin ya faru a Jihar Kano ya mayar da hannun agogo baya wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a cikin jihar, kuma ya warware duk wata yarjejeniyar da aka kulla, wajen yin zabe a bisa zaman lafiya da lumana, da yin zabe a bisa tsabta.

Muna amfani da wannan dama domin yin kira ga al’ummar Jihar Kano cewa su dubi yiwuwar rungumar zaman lafiya da kaunar juna a tsakaninsu, domin farfado da martabar jiharsu da kuma kimar wannan yankin namu na Arewa mai albarka.

Muna fatan hukumomin tsaro a Jihar Kano za su yi binciken kwakwaf domin zakulo mutanen da ake zargin suka aikata wannan aika-aikar hadi da wadanda suke da sa hannu wajen aukuwar lamarin domin hukunta su daidai da abin da suka aikata, domin hakan ya zama izina ga masu kokarin aikata makamanciyar irin wannan ta’asar.

Muna fatan Allah Ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano da Arewacin Najeriya baki daya.

Daga Nura Muhammad Mai Apple, Gusau 08133376020.