✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasar Najeriya ko saye da sayarwa?

Anyi siyasa ta kishin kasa da al’umma, mulkin tsaro na rayuka, lafiya, dukiya, mutunci da addinin kowa da kowa. A lokacin su Dr. Nmandi Azikwe,…

Anyi siyasa ta kishin kasa da al’umma, mulkin tsaro na rayuka, lafiya, dukiya, mutunci da addinin kowa da kowa. A lokacin su Dr. Nmandi Azikwe, Alh. Sir, Abubakar Tafawa Balewa, Chief Obafemi Awolowo da Sa Ahmadu Bello, J.S. Tarka, Malam Aminu Kano da saurensu. Da a ce Cif Obafemi Awolowo da Malam Aminu Kano suna da rai, Janar Olusegun Obasanjo bai isa ya yi mulkin siyasa/farar hula ba, ballantana har wasu sojojin su rika yin rububin su gaje shi, har ma a jihohi wai sojoji su rika fafutukar su zama gwamnoni, ko su zama kwamishinoni a jihohi da makamantan wadannan. Musamman wadanda aka san sun taba yin juyin mulki, suka yi sata, kowa ya gani. Uwa uba suka rusa kasar ta fannin tsaro, tattalin arziki da siyasa, irin su o.o! A gabana Chief Obafemi Awolowo ya ce, a gare shi komai lalacewar mulkin Dimokaradiyya yafi mulkin soja, komai kyawunsa. A lokacin da aka yi masa magudin zabe a 1983. Ya ce idan Shehu Aliyu Shagari bai gode wa Allah tsawon shekaru hudu da ya yi yana mulki ba, ya ci gaba. Yayinda Alh. Shehu Shagari har Papa Roma ya gayyato, ya shafa masa kai, ya hada shi da Kiristocin Najeriya don su zabe shi, bacin ya je kabarin J.S. Tarka, ya fito da tattabaru adadin yawan jihohin Najeriya na lokacin daga cikin buhu, wajen yakin neman zabe. Duk da haka sai da aka yi magudin zabe da ba a taba yin irinsa ba, sannan aka ce Shagari ya lashe zaben. Shi ne abin da ya haifar da maganar Cif Awolowo, wata uku a tsakani aka yi juyin mulki, aka tsare Shagari har tsawon watanni 20. 

Har yanzu sojoji ne ke da tasiri kan siyasar Najeriya saboda kudin sata da irin yaransu da suka dasa ta yadda suka ci gaba da mulki yadda suke so. Idan anji haushi a zazzage kowanne soja da ya yi mulki, za a ga abin da ya mallaka da irin yaransa da suke kula masa da dukiyar manaa. Tun daga lokacin da Shagari da ya ba da kafa sojoji suka karbi iko suka kwace mulkin, shi ne muke fama da kowacce irin annoba, wani abin na ban mamaki, hatta rikicin Marwa Mai tatsine da Alh. Shehu Shagari ya kafa kwamiti na mai shari’a Anyagulu ya bincika, har aka yi masa juyin mulkin bai yi koma a kan sakamakon binciken ba, wadanda suka biyo bayansa har izuwa yanzu (1980 – 2014). Abin sai ma kara muni ya yi. Shine nake tunawa da waccan magana ta Chief Obafemi Awolowo da magudin da aka yi masa ya hakura don kada sojoji su sami damar komawa kan mulkin, duk da kasancewarsa Minista na kudi a mulkin Janar Yakubu Gowon. Kamar yadda Mal. Aminu Kano yana Ministan Sadarwa ya sauka saboda bai gamsu da mulkin Janar Yakubu Gowon ba, dama saboda hadin kan kasa suka shiga gwamnatin, karshe suka fahimci tsarin soja ba irin na dimokuradiyya ba ne.
Da aka tambayi Mal. Aminu Kano, me ya koya a cikin gwamnatin soja? Sai ya ce sun koyi idan sun gani sai a hana su fada. Da Gowon ya nemi ya zarce, su suka tadiye shi, bai kai labari ba. Kamar yadda muka hana IBB, Sani Abacha da OBJ. Sai ga shi mun yi baya ba zani, aka wayi gari duk wadanda suka gaje su har a jihohi yaransu ne.
Yanzu dai kowa yanaji yana gani anata kashe mutane, ana satar mutane da dukiyar kasa ba dare ba rana, har ta kai an kama jirgin Shugaban kungiyar Kristocin Najeriya a Afrika ta Kudu makare da kudi tsaba, har Dala miliyan tara da dubu 300 ($9.3m) da ’yan Najeriya biyu, da dan Isra’ila daya, sai shugaban kasa Ebele Jonathan ya fito fili yana cewa gwamnatinsa ce ta aikesu da kudin don sayo mata makamai. Ba fa tare da wani jami’in tsaro na Najeriya ba, ba a jirgin Soja ko na Shugaban kasa ba, ba tsakanin gwamnati da gwamnati ba, ba daga banki zuwa banki ba, a a ta barauniyar hanya. A kashe suwa da wa??? Tun kafin wannan ta faru wani Bature dan Austireliya da aka gayyato don shiga tsakani da kungiyar Boko Haram su saki ‘yan matan makarantar Chibok 276 da suka yi garkuwa da su, Baturen ya tabbatar tsohon Gwamnan Jahar Borno Sanata Ali Modu Shariff da tsohon Shugaban Sojojin Najeriya Janar Ihejirika ne suke tallafa wa kungiyar ta Boko Haram.
Kafin duk wannan tsohon mai bada shawara akan tsaron kasa (NSA), Janar Azazi yace, PDP ce take tsara yadda aketa kashe mutane, karshenta shima aka kashe shi ko ya mutu. Tsohon Shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Jonathan wasika mai shafi 18, inda ya zarge shi da tsara kashe mutane dubu, har yau ba’ayi wani abu akai ba. Sai hare-hare da ake ta kaiwa a wasu makarantu da sauransu na Arewacin Najeriya. Ga maganar kudin da aka kama a Afrika ta kudu a jirgin Shugaban kungiyar Kristocin Najeriya.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya taba kokawa kan kudin kasar nan $49.8bn na cinikin gurbataccen mai, da ba’a shigar CBN ba, aka yi ta ja-inja har aka soma shigo da wasu, saura $20bn har yanzu babu labarinsu koma irinsu ne aka kama!
Sai makomar Najeriya a irin wannan yanayin da ake, ko dai ‘yan majalisar tarayya masu ikon tsige shugaban kasa suyi maza su tsige shi, idan ba tare suke aikata duk abinda yake faruwa ba, kamar na N2.7 triliyan na tallafin mai da aka bai wa Faruk M. Lawal $600,000 suka yi shiru da maganar, yanzu kuma ana cewa an fara bai wa wasunsu $20,000 zuwa $50,000 kada su yi bincike akan $9.3m da aka kama a Afrika ta Kudu a cikin jirgin Fasto Ayo Oritsejafo, shugaban kungiyar kristocin Najeriya (CAN). Ko kuma dukkanin shugabannin kowanne addini wadanda ba su da hannu akan kashe-kashe da sace-sace da ake ta yi mana su zo mu hadu, tare da dukkanin mabiyansu da talakawa da ake zalunta, kowa ya zo mu hada kai, mu tilasta wa ‘yan majalisar tarayya da duk wadanda aka zaba, su sauka, a kafa gwamnatin rikon kwarya, wacce za ta binciki kowa da komai, akan dukkanin abubuwan da suka faru, ta hukunta duk wanda aka samu da laifi. Koda ya zama dole ne sai an canza kundin tsarin mulkin na Najeriya. Kamar dai yadda aka tilasta wa IBB da OBJ suka hakura suka sauka. Duk wata doka komai karfinta, idan ba dokar Allah ba ce, yawan mu ya fita karfi.
Makasudin kafa kowacce irin gwamnati a ko’ina a duniya shi ne: kare rayuka, lafiya, dukiya, mutunci da addini na duk ‘yan kasa har ma da baki, wanda ba mu da ko daya. Saboda haka ya zame mana dole mu tashi tsaye munema wa kanmu dukkan wadannan abubuwa na wajibi, guda biyar. sai ga wasu $5.7mil an sake kamawa a dai Afrika ta Kudu, za’a sayo makamai, hatta wasu daga manyan Kristocin Najeriya irin su Sanata Akume da irin su Kaigama sai da suka fito fili suka la’anci shugaban kungiyar CAN akan wannan badakala, wasu kasashen na duniya irin su Amurka sun yi tofin Allah ya tsine da wannan abu da ya faru da sunan masu mulkin Najeriya, amma wasu dattijai na Arewa, musulmi saboda kwadayi sun tare a fadar Jonathan duk abin da ya yi suna tare da shi.
Firayiministan Ingila ko Jirgin gwamnati ba shi da shi, sai Shugaban kungiyar Kristocin Najeriya, tilas ne duk yadda za a yi a rusa majalisar kasa, a kafa gwamnatin rikon kwarya mai cikakken iko ta bi mana kadin dukkan abubuwan da suka faru tun daga 1979 zuwa 2014. Musamman kan abin da ya shafi tsaro da tattalin arziki da siyasa. Kamar yadda Allah ya yi umarni a yi kotuna da alkalai da kurkuku da ‘yan doka da sauran jami’an tsaro na kwarai, adalai domin a hana laifuka, a hukunta masu kowanne laifi. Kafin mu dunguma gaba daya zuwa lahira, inda babu maganar saye da sayarwa da wasu ke yi na mutunci ko martaba da Allah ya yi musu suka banzatar da su a duniya. Za mu tsaya tare gaban Mahaliccinmu, mai kowa mai komai, Allah (S.W.T), inda za a yita ta kare. Da fatan Allah ya sadamu da rahamarsa, amin!

Abdulkarim dayyabu
Shugaban Rundunar adalci ta Najeriya
08023106666, 08060116666