✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sufeto Janar ka bai wa marada kunya

“Duniya ta fi bagaruwa iya jima”. Ina magana akan nadin da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa Suleiman Abba a matsayin sabon mukadashin sufeto Janar…

“Duniya ta fi bagaruwa iya jima”.
Ina magana akan nadin da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa Suleiman Abba a matsayin sabon mukadashin sufeto Janar na ‘yan sandan kasar mu Najeriya. A ranar 1 ga watan Agustan 2014. Wanda shakka babu wannan dori nasa ya doru a daidai da gabar da ke daf da karyewa bayan fama, da gwabje-gwabjen da ta sha yi. Kuma muna fatan Suleiman Abba zai samo madoran asalin, domin rigakafi, wanda Hausawa suke cewa ya fi magani. Domin maganar gaskiya tsohon sufeto janar din da ya gada, ya aikata mummunar aika-aika a hukumar ’yan sadan Najeriya a tsawon mulkinsa na shekaru biyu da kwana 19. wanda tabbas dinke wannan baraka, sai jarumin kwarai.
Lallai akwai bukatar sabon sufwto janar din ya yi kokarin bai w amara da kunya, wajen tunkarar mtsalolin da suka addabi ’yan sanda, ta yadda za su ji dadin tafiyar da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan. Kuma su himmatu wajen kauce wa cin hanci da rashawa.
Domin kwata-kwata MD Abubakar bai bar wa hukumar ’yan sandar kasar mu wani kyakkyawan tarihi ba. Tun daga ranar da aka ruwaito Sulaiman Abba ya maye gurbinsa, ’yan siyasar kasarmu manya da kananansu suke ta tofa albarkacin bakinsu akan cancantarsa, a wannan mukamin kamar yada shahararren  dan gwagwarmaya, Injiniya Buba Galadima ya fada a kafar yada labarai ta BBC, a ranar 1-8-2014 da cewa ya san Mista.Abba shekaru 30 da suka shude yana daya daga ’yan sanda masu kwatanta adalci. Su kuma ’yan sandar kasar muke ci gaba da murnar da doki a kan raba su da kayar da Allah ya yi. Saboda da irin mulkin malaka’un da MD Abubakar ya yi musu tare da tauye wa manya da kananan’yan sandar kasar hakkokinsu, musamman a watan azumin shekara 2013, inda aka debe wa kowane dan sanda Naira 11,000. Wanda wannan zalunci ne muraran.
Kuma a bangaren mu farar hulla abun ba a ma magana domin a lokacin mulkin MD Abubakar an samu karuwar tashe-tashen hankulan da rashin tsaron da ba a taba tsammanin za a samu ba. Tare da ƙaruwar gungu-gungu na jami’an ’yan sanda da ke tare manya da kananan hanyayoyinmu da sunan samar da tsaro. Wanda wallahi,ba shi ne su ke mai da hankali a kai ba illa dai su karbi na goro ga duk mai motar da sunka raina kurarsa da ma fasinjan da ya dauko, wanda duk  wani mai motar da ke biyar hanyoyin kasar a kullum ya cikin neman canjin rabama ’yan sanda. Wanda duk rashin kyakkyawan jagoranci ne ya kawo haka. Domin rashin tsawatarwa  da hukunci shi ne babban abun da ya kawo hakan. Inda yanzu har an wayi gari sun mai da amsar Na-goro tamkar shi ne an ka dauke su aiki su yi, wanda har an wayi gari su ke dauƙar matakai iri-iri ga duk wanda ya hana masu,waya alla ko dan bai da abun ba su ne ko akasin hakan, matakan da sunka kama daga tozartarwa,duka dama kazafin aikata laifin ba gaira balle dalilin yinsa.
Allah mai yadda ya so! Hausawa kuma suke fadin “duniya rawar ’yan mata” to yau an wayi gari MD Abubakar ya bar wannan mukamin bari na har abada. Sulaiman Abba wannan ma abin ishara ne a gareka, domin kai ma za a wayi gari  ka wuce, kamar yadda shi ma ya wuce,ko dai
lokacin da aka dibar maka ya cika ka sauka, ko ma dai me ye wallahi sai an wayi garin ba kai ne a Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya ba.
Don haka shawararmu daya gare ka, ka yi duk mai yiyuwa wajen kwatanta adalci, wanda adalcin dai ne zai cece ka gaban Mahaliccin kassai da sammai. Haka Kuma adalcin dai ne zai sa al’ummar Najeriya su so ka, tare da yi maka fatan karewa da duniya lafiya. In kuma ka yi akasin hakan, to, wannan ruwanka, domin yadda ka ga muka rubuta wa tsohon mai gidanka, haka kai ma za mu rubuta  irin nau’in jagorancinka.
Daga karshe muke rokon Allah ya baka ikon kwatanta gaskiya da adalci a lokacin jagorancin wannan hukuma ta ka, ya Allah muna rokonKa ka sanya wannan jagorancin naka ya zama shi ne jagoranci mafi tsafta, kuma shi ne zai za ma sanadiyyar tsaftace hukumar ’yan sandan kasarmu Najeriya, Allahumma amen.
AbdulMalik Saidu Mai Biredi, Tashar Bagu Gusau 08069807496.