✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Suleja: An dawo da jaririyar da aka sayar a Anacha

An dawo da wata jaririya ’yar wata biyu da ake zargin mahaifiyarta ta sayar da ita a kauyen Chaza da ke wajen garin Suleja ta…

An dawo da wata jaririya ’yar wata biyu da ake zargin mahaifiyarta ta sayar da ita a kauyen Chaza da ke wajen garin Suleja ta jihar Neja ranar Talatar da ta gabata, bayan an kai ta garin Anacha ta jihar Anambra inda aka sayar da ita a kan kudi Naira dubu 150.
Shugaban kungiyar ’yan sintiri na kauyen Chaza Malam Bisalla Akoshi ne ya bayyana wa Aminiya haka a ofishinsu.
Malam Bisalla Akoshi ya bayyana cewa wanda ake zargi da sayan jariyar ne, wani dan kabilar Ibo da ke sana’ar tagogi da kyamare na alminium a Abuja, mai suna Baba Amala, ya sanar da su. Baba Amala wanda yake zaune a Unguwar Kashu a kauyen na Chaza, a yayin bincike da kansa ya sanar da su cewa shi ne ya aikata laifin, inda ya sanar da su cewa ya sayi jaririyar ne a dalilin jinkai. Ya ce mahaifiyarta, wadda ’yar kabilar Tibi ce daga garinn Makurdi a Jihar Binuwai, wadda kuma take zaune a kauyen, ta koka a kan matsalar rayuwa da ta samu kanta, musamman ta bangaren kulawa da jaririyar.
 Shugaban ‘yan sintirin ya ce, wanda ake zargin ya shaida musu cewa, ya sayeta ne don aikawa da ita zuwa wajen kanwarsa da ke garin Anacha (Onitsha) don renonta, kasancewar Allah bai ba ta haihuwa ba bayan ta yi aure kimanin shekara takwas, inda matarsa da ake kira Mama Amala ta kai ta wurin ‘yar uwar tasa. Sai dai bayan bayyanar al’amarin, Baba Amalan sai ya umarci matar tasa da ta dawo da ’yar, ta kuma dawo da ita a ranar Talatar da ta gabata.
Har  zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu nasarar kama uwar jaririyar ba, inda bayanai suka nuna cewa bayan ta amshi kudin ta wuce garinsu ne inda ta ce za ta yi amfani da kudin a matsayin jari. Sai dai ana tsare da wadansu mutane uku, baya ga Baba Amalan, wadanda aka tsaren sun hada da wata mai suna Ebelyn, ’yar asalin yankin kudancin Kaduna da ke matsayin uwar dakinta tare da kasancewa a matsayin wadda ta yi dillacin jaririyar a tsakanin uwarta da kuma wanda ya saye ta.
 Sai kuma wata mai suna Aghatha Maduako da ta zauna da uwar jaririyar a gida guda a lokacin da take tare da wani saurayi, bayanai sun nuna cewa Aghatha ce ta gabatar da matar a Majami’ar Katolika na kauyen inda ta rika zuwa sujada. sai kuma wani mai suna Odaji, wanda ke matsayin saurayinta na baya-bayan nan kafin daga bisani ya kore ta bayan sun samu sabani. tuni dai jami’an ’yan sintirin suka mika mutanen hudu ga babban ofishin ’yan sanda na “B” Dibision da ke Suleja inda ake ci gaba da bincike.
 Aminiya ta samu bayanin cewa uwar jaririyar  ta haifar wa wani Soja jaririyar ne, sai kuma ’yarta mai shekara biyu, ita kuma ta haifar wa wani dan sanda, kuma ubannin yaran biyu sun yi watsi da ita ne daya bayan daya. Haka nan bayanin ya nuna cewa shi ma saurayin nata na baya-bayan nan da ke cikin wadanda ake binciken, mai suna Odaji ya yi watsi da ita, kuma a sanadin hakan ne ta gabatar da kanta ga cocin Katolika na kauyen Chaza, inda ta sanar da su bukatarta na komawa gida Makurdi.
A bayanin da ya yi wa wakilinmu, babban jami’in kudi na mujami’ar mai suna Christian Ayo, wanda ya yi bayani a madadin Fada na Mijami’ar, ya bayyana cewa da hannunsa ya ware kudi Naira dubu biyar ya bai wa matar, bayan mijami’ar ta amince a taimaka mata da kudin, kamar yadda ta bukata don komawa gida. Sai dai ya ce bayanin da ya ji daga bisani shi ne ta sayar da Jaririyarta ga wani gabanin ta bar garin.
Lokacin da Wakilinmu ya tuntubi babban ofishin ’Yan sanda na “B” dibision Suleja a ranar Laraba da ta gabata, an sanar da shi cewa babban Jami’in ’Yan Sanda na Ofishin (D.P.O) ya je garin Minna don gabatar da aikace-aikacen da ofishin ya gudanar.
 Da Aminiya ta tuntubi babban Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, A.S.P Richard Adamu, ya bayyana cewa ba shi da masaniya a kan al’amarin.