✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci: Abin da ke faruwa a Nasarawa daya ne da na Yobe da Borno – Labaran Maku

Tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APGA Mista Labaran Maku ya tattauna da wakilinmu game da rigingimun kabilanci a…

Tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APGA Mista Labaran Maku ya tattauna da wakilinmu game da rigingimun kabilanci a jihar da kuma shari’arsa da Gwamna Al-Makura da sauransu kamar haka:

Me za ka ce game da karuwar rigingimu da kuma ta’addanci a jihar nan?
Da farko zan so in bayyana bakin cikina dangane da abubuwa da suke faruwa a jihar nan a shekara uku na shugabancin Gwamna Umaru Tanko Al-Makura. Tunda ya hau mulki jihar nan tana ci gaba da fuskantar bala’o’i daban-daban. Yau ayyukan ta’addanci sun mamaye jihar nan baki daya. Babu wani bambanci da abubuwa da suke faruwa a jihohin Yobe da Borno da sauransu a Arewa maso Gabas. Rigirgimun kabilanci da suke faruwa a da yanzu an mayar da su na ta’addanci kuma duk kananan hukumomin da muke da su a jihar nan lamarin yana shafarsu. Kowa ya san cewa wadanda suke kashe mutane a jihar nan an yi hayarsu ne daga wani waje ba ’yan jihar nan ne ba. Su kansu ’yan ta’addan suna fadin haka. Kuma a kullum muna addu’a Allah Ya tona asirinsu don babu bako da ba za ka ji an kashe mutum ba a jihar nan. Tsakanin lokacin zaben bana na watan Afrilu zuwa yanzu an kashe sama da mutum 100 a jihar nan. A wasu kauyuka da ke garuruwan Kadarko da Kiyana ma a ’yan kwanakin nan mazauna wadannan kauyuka sun wayi gari wata rana suka ga wasu ’yan bindiga suna shiga musu kauye inda kafin su san abin da ke faruwa sai ’yan bindigar da yawansu suka soma bude musu wuta har sai da suka kashe sama da mutum 70 ba gaira ba dalili. Kuma galibin wadanda aka kashe mata da yara ne. Kuma har yanzu da muke magana gwamnati ba ta ce komai ba, duk da cewa na ji cewa Gwamna Al-Makura ya ziyarci kauyukan bayan aukuwar lamarin. Bayan wannan kuma al’ummomin Migilli da Daddare da Obi an bi su har gonakinsu inda aka yi wa yara da matansu yankan rago. Babu wanda aka kama har yanzu. Haka kuma cikin mako uku da suka gabata wasu ’yan bindiga sun kashe mutane da dama a kan hanyar Agwada zuwa Nasarawa. Wadannan mutane suna kan babura ne ’yan ta’addan suka harbe su. Hai ila yau babu ranar da ba a kashe mutane a kauyukan Odeni Magaji da sauran kauyukan yankin. Al’ummomin wadannan kauyuka tuni sun daina zuwa gonakinsu kwata-kwata sakamakon ayyukan wadannan miyagun mutane. Kuma wuraren nan ne kamar yadda ka sani jihar nan ke alfahari da su wajen samun albarkatun gona. Sai aka wayi gari a gwamnatin Al-Makura harkokin ta’addanci suka mamaye su baki daya. Ana lalata da mata da ’yan mata a idon iyayensu kusan kullum. Kuma kamar yadda na bayyana wadannan ’yan ta’adda ba ’yan atalin jihar nan ne ba ana yin hayarsu ne daga wajen jihar. Shi ya sa a lokacin da nake Ministan Tsaro na turo sojoji jihar nan, bayan na sanar da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yanayin rashin tsaron jiharmu musamman a kan manyan hanyoyi. Yanzu da aka cire shingayen sojoji lamarin yana kara muni. Na tabbata ba a sanar da Shugaban kasa Buhari yadda lamarin tsaro yake a jihar nan ba. Da an sanar da shi da ba zai yarda dokar ta shafi jihar nan ba. Don bayan jihohin Yobe da Borno sai jihar nan idan ana maganar jihohin da harkokin ta’addanci suka fi yawa ne. Batun talauci da cin hanci da rashawa a jihar nan kuwa sai gwamnati mai ci yanzu ta tattara nata ta kara gaba kafin a magance su.
A ’yan kwanakin nan gwamnatin jihar nan ta kirkiro da doka cewa ma’aikatanta su rika biyan kudin haraji daga albashinsu kowane wata. Kana ganin hakan zai haifar da da mai ido?
Ka ga idan akwai adalci a gwamnati kowa zai so ya ba da tasa gudunmawa don ya tabbata za a yi amfani da kudin yadda ya kamata. Amma a jihar da gwamnati take kashe sama da Naiar miliyan 100 kowane wata a matsayin kudin tsaro kuma babu tsaron kuma maimakon ci gaba sai ana ta yin hayar ’yan ta’adda ana kashe mutane a gidajensu da gonakinsu da sauransu. Ka ga wannan doka ba za ta yi tasiri ba. Saboda haka wadannan kame-kame da yake yi (Al-Makura) ba za su taimake shi ba. Kuma kamar yadda na bayyana dokar ba za ta yi tasiri ba. Ai ma’aikatan gwamnatin ba jahilai ba ne da zai zo ya ce musu su cire haraji daga kalilan kudin da yake ba su a matsayin albashi.
Kana nufin ya kamata Hukumar EFCC ta gudanar da bincike a gwamnatinsa ke nan?
Ni ba haka nake nufi ba. Ni ban taba gayyatar wata hukuma ta binciki wani ba. Don bai aikina ba ne in yi haka. Idan EFCC ta ga ya dace ta tuhume shi aikinta ne babu ruwana. Amma abin da nake fadi shi ne al’ummar jihar nan suna so a nada ainihin wanda ya ci zabe ne a matsayin gwamnansu. Kowa ya san cewa ni na lashe zaben Gwamna da ya gabata a jihar nan. Amma Al-Makura tare da da hadin kan hukumar zabe suna so su kwace mini. Kuma na sha alwashin cewa ba za su iya yin haka ba. Har yanzu al’ummar jihar nan suna cewa “Ba mu zabi Al-Makura ba, me yake yi a gidan gwamnati?” Saboda haka ina so in tabbatar maka cewa ina da damar cin nasara a kotu don kwace mulkina da yake so ya sace min.
Misali idan ta ikon Allah kotu ta bayyana ka a matsayin ainihin wanda ya lashe zaben Gwamnan. Me za ka yi ga al’ummar jihar nan?
Ka ga da farko ina siyasa a jihar tun 1999. Na rike Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida. Na kuma rike mukamin Mataimakin Gwamnan Jihar nan a lokacin Abdullahi Adamu. Saboda haka na san matsalolin jihar nan ciki da waje. Shi ya sa ma na yanke shawarar tsayawa takarar. Akwa wasu kungiyoyin tabbatar da zaman lafiya da dama da na shugabance su a jihar nan. Kuma na kawo zaman lafiya a tsakanin al’ummomin jihar nan da a da ba sa iya kallon junansu. Na yi haka ne ta hanyar sulhunta su. Saboda haka a takaice dai idan na samu nasara a kotu wanda na kuma tabbata zan samu zan fara ne da sasanta al’ummomin nan da ke fada da juna. Sannan in fuskanci wasu ayyuka. Lokaci ba zai ba ni damar bayyana maka abubuwa da zan gudanar ba idan na samu nasara. Wadannan kadan ne kawai daga cikinsu.