✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyya

Wani Bafulatani ne aka yi masa mutuwa sai wasu abokansa uku suka zo ta’aziyya. Na farko ya ce: “Ashe baffa Allah ya yi masa rasuwa?…

Wani Bafulatani ne aka yi masa mutuwa sai wasu abokansa uku suka zo ta’aziyya. Na farko ya ce: “Ashe baffa Allah ya yi masa rasuwa? Allah jikansa.” Na biyu ya ce: “Ashe baffa Allah ya yi masa mutuwa? Allah gafarta masa.” Na uku ya ce: “Ashe baffa kwana ya kare? Allah rahamshe shi.” Bayan sun tafi sai ya fashe da kuka ya ce: “Baffa abin ya yi masa yawa, ga mutuwa ga rasuwa ga karar kwana! Allah sa su tambaye shi daya kawai.” 

Daga danladi China Kano, 08034463170