✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talla Jami’a ce ta lalata tarbiyyar mata – Hajiya Zariyatu Hashidu

Tarihina: Sunana Hajiya Zariyatu Abubakar Hashidu,  an haife ni a garin Maiduguri tun a tsohuwar jihar Arewa North Eastern State a ranar 18 ga watan…

Tarihina:

Sunana Hajiya Zariyatu Abubakar Hashidu,  an haife ni a garin Maiduguri tun a tsohuwar jihar Arewa North Eastern State a ranar 18 ga watan Fabarairu shekarar ta 1974, a lokacin iyayena suna can da aiki, a shekara ta 1976 suka dawo Jihar Bauchi, amma kuruciyata ta a garin Yola na yi lokacin tana tsohuwar Jihar Gongola.  A can na yi karatun Nursery da Firamare ta Capital School da Sakandaren ’yan Mata ta gwamnatin tarayya da ke Yola FGGC.   Na gama a shekarar 1990.  A shekarar 1991 na tafi Jami’ar Maiduguri na yi Digiri na farko a bangaren harkar kasuwanci wato Business Management (Marketing) da na gama sai na tafi yi wa kasa hidima na shekara daya inda aka tura ni Jihar Osun amma saboda ina da aure da karamin yaro sai aka mayar da ni inda maigidana yake aiki a Jos ta Jihar Filato inda na yi hidima ta a gidan talabijin na NTA, bayan na gama NYSC sai na kama harkar kasuwanci gadan- gadan tun da abun da na karanta ne, da na yi shekara biyu sai na fara aiki da wata kungiyar da ba ta gwamnati ba (NGO) inda nake daukar wani kaso na ribar kasuwancina ina taimakawa mata da kananan yara marasa lafiya da kudin magani a asibiti, da yake maigidana Likita ne har ta kai ya gane ina wannan taimakon a wani lokaci idan aka kawo marar lafiya ya kasa biyan kudin magani sai ya gaya min sai na biya musu da haka har shi ma ya ci gaba da goya min baya kan wannan taimako da nake yi. Wannan tallafi da nake bayarwa ne mutane suka ba ni shawarar na kafa kungiya mai zaman kanta wacce ba ta gwamnati ba NGO, shi ne a shekarar 2007 na kafa kungiya mai suna Wildan Care Foundation, da muke taimakawa mata da yara marasa lafiya da gajiyayyu  har ma da bangaren karatun su.

 

Aiki:

Na fara aiki ne da Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya  FCE (T) da ke Gombe  bayan na daina harkar kasuwanci a shekara ta 2010 har zuwa yau kuma ina jin dadin yadda dalibai na suke ba ni hadin kai a lokacin da nake aji ina koyarwa.

 

Nasarorin da na samu a rayuwa:

Gaskiya na samu nasarori da yawa domin a dalilin wannan koyarwa da na ke yi na samu dama na karo karatu domin da Digiri daya nake da shi ina koyarwar na samu tafiya na yi babbar Difloma wato PGD sannan yanzu haka na kammala digiri na biyu (Masters), kuma in Allah Ya yarda kafin karshen wannan shekarar zan tafi yin digiri na uku wato Phd, wanda da ba don aikin ba da watakila har yanzu digiri di na daya. Har ila yau kuma wata nasarar ita ce kasancewa ta Malama ina samun kulawa ta musammam daga dalibai na domin ko banki na shiga ko wani abu zan yi a cikin gari sai na ji an ce Malama bari na yi miki, sai in ga an tayani idan na tambaya sai mutumin ya ce min ai shi dalibi na ne a Kwaleji.

 

Kalubalen da na fuskanta:

Kalubale akwai shi a rayuwa amma da yake na samu tallafi da kulawar iyayena kalubalen ya zo mini da sauki domin haka kuma shi ma maigidana Dokta Alkali ya taimaka mini sosai wajen shawo kan wasu matsaloli na rayuwa kasancewar na yi aure ne a lokacin da nake jami’a. Wani abu da ya sa nake ganin kalubalen bai kai kalubale ba shi ne na yi koyi da mahaifiya ta lokacin tana First Lady duk wani aikin gida da ya shafi na mahaifina lokacin yana gwamna ita take yi da kanta ba ’yar aiki ba hatta abinci ita take masa shi ya sa ni ma na koyi wasu abubuwa daga wajen ta. Idan na tashi da safe zan yi kokari na yi duk wasu ayyukan da suka kamata kamar hada abincin karyawa da na rana in saka a flask in ajiye wanda ko maigidana da yarana sun dawo da rana ba na nan abincinsu yana ajiye za su dauka su ci kafin na dawo.  Babban kalubalen da wasu mata suke dauka na hada rainon yara da aikin gida da kuma na ofis ka ga ni bai zama min kalubale ba tun da ka ga yadda nake yi na shawo kan al’amarin har yanzu kuma haka nake yi shekara 25 da yin aure na ban taba gajiya wa ba wanda kuma hakan shi ne sirrin zamana lafiya a gidan aure na.

 

Yadda na hadu da maigidana:

Maigidana dan Karamar Hukumar Dukku ne iyayena ma ’yan Dukku ne amma garin mu shi ne Hashidu, akwai kuma alaka mai karfi tsakanin gidajenmu wato a tsakanin iyayena da iyayensa.

 

Tufafin da na fi sha’awa:

Nafi sha’awar in dinka doguwar riga mai dogon hannu in yafa gyale. Haka kayan kanti ma ina sanyawa su ma doguwar riga  wanda duk wanda ya ganni zai mini kallon mutunci kuma da ka ganni ka ga ’yar arewa cikakkiya. Yana da kyau mu yi riko da al’adunmu na gargajiya.

 

Kasashen da na taba zuwa:

Na je Ingila da Amurka da Saudiya ba adadi . Na je Dubai nan ma ba adadi.  Na je Suwizilan da Jamus da Sweden da sauran kasashen da ba zan iya lissafawa ba.

 

Kungiyoyi:

Ina da kungiya mai suna Wildan Care Foundation da Women International For Peace and Freedom, (WILPF) da MSCH Coalition da Association for OBC