✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin mai ba ya tallafar talaka – kungiyar IPMAN

Alhaji danladi Garba Pasali shi ne  Sakataren kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN). A wannan tattaunawar ya  bayyana fahimtarsa game da janye tallafin da…

Alhaji danladi Garba Pasali shi ne  Sakataren kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN). A wannan tattaunawar ya  bayyana fahimtarsa game da janye tallafin da aka yi kamar haka:

 Alhaji Danladi Garba PasaliAminiya; Wane tasari ko kuma rashinsa kake ganin wannan janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi  zai kawo a kasar nan?
danladi Pasali: Wato abin da za mu gane dangane da wannan al’amari na janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi shi ne, yau Nijeriya ta shiga wani mawuyacin hali na rashin kudi, domin rayuwarmu ta dogara ne da danyen man da ake fitarwa zuwa kasuwar duniya don sayarwa.  Yanzu farashin wannan danye mai ya fadi a kasuwar duniya. Don haka  kudaden shiga da suke shigo mana sun yi kasa. Saboda haka dalar da zamu tara mu ce za mu je mu sayo man fetur a waje yanzu babu. Kuma kudaden da ake da su a da duk an sace.
Gaskiyar magana, cire tallafin man fetur yanzu a kasar nan shi ne ya kamata. Domin wannan tallafin mai  wadansu mutane  ‘yan kalilan ne  suke amfana da shi. Talakan kasar nan ba ya amfana da tallafin man nan. Domin man nan da ake magana a manyan biranen kasar nan kamar Abuja da Legas da Fatakwal da Warri ne kawai ake sayarwa kan farashin gwamnati. Amma sauran garuruwa da kauyukan kasar nan  ba a sayar da man kan farashin gwamnati. Kusan shekara 2 ko 3 abin da ake fama da shi ke nan a kasar nan. Kuma maganar tallafin man fetur  ya zama wata hanya ta wawure kudaden kasar nan.
Don haka cire wannan tallafi ya yi daidai, domin  zai bai wa ‘yan kasuwar duniya dama  su shigo kasar nan,  su bubbude matatun mai masu zaman kansu. Kuma maganar tashin farashin man zai kasance yanzu ne kawai, amma nan gaba zai iya fadowa kasa. Domin an ce kowa ya je ya kawo man fetur din nan, da zarar man fetur din nan ya fara shigowa dole ne farashinsa  zai iya faduwa kasa.
A da a cikin kamfanonin da ake da su a kasar nan wadanda suke shigowa da man fetur,  kashi 20 kawai ake  bai wa dama su je su shigo da shi. Kuma bayan haka an dinga bin wadansu hanyoyi na rashin gaskiya da cin hanci, kafin a je a shigo da man nan.  Amma yanzu tun da  an ce an bude kowa yaje ya kawo man, ya zama kasuwa ke nan. Don haka ina mai tabbatar maka mu ‘yan kasuwa idan man fetur dinmu ya fara zuwa, ba za mu sayar Naira 140 ba, za mu sayar kamar Naira 120. Saboda haka ina mai tabbatar maka cewa idan ‘yan kasuwa suka fara kawo man nan dole ne farashinsa ya fadi, saboda wannan ya kawo wancan ya kawo, kuma kowa yana son ya sayar ne.
Irin wannan ta faru da man dizel, yanzu mutane da yawa ba sa sayen man dizel a NNPC, sun gwammace su je su saya a gidajen mai na ‘yan kasuwa saboda ya fi araha. Saboda a NNPC ana sayar da lita kan Naira 130 ne, amma a gidajen man ‘yan kasuwa akwai wadanda suke  sayar da lita har Naira 100.

Aminiya; Wato a takaice wannan mataki da aka dauka na janye tallafin man fetur yana da tasiri a kasar nan?
danladi Pasali: Yana da tasiri, domin zai taimaka wa kasar nan. Saboda gaskiyar magana, tallafin man fetur wata hanya ce ta cin hanci da rashawa a kasar nan. Kuma wadansu ‘yan tsiraru ne suke amfana.  Domin a cikin kananan hukumomin kasar nan 774 idan ka duba wadanda suke sayen man fetur kan farashin gwamnati ba su fi kashi goma na al’ummar kasar nan ba.

Aminiya; Wane kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar kasar nan dangane da wannan al’amari?
danladi Pasali: Ina kira ga jama’a su yi hakuri su ba da dama kan wannan al’amari zuwa nan da wata 1 ko wata 2. Wannan abu da yake faruwa kamar kungiyoyin kwadago da sauransu, a yau an wayi gari matatun man kasar nan ba sa aiki kuma da ma’aikatan kwadagon nan ake bata wadannan matatu. Domin suna kallo ake sace kudaden kasar nan, amma ba su dauki wani mataki ba. Tun da  yanzu da Allah Ya bamu shugaba mai adalci da gaskiya, wanda yake da burin kawo gyara a kasar nan, mu yi hakuri mu ba shi goyan baya.