✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tanzaniya ta yi afuwa ga fursunoni 5000

Shugaban Kasar Tanzaniya, John Magufuli ya yafe wa fursunoni sama da dubu biyar a bikin tunawa da cika shekara 58 da ’yancin kan kasar Tanzaniya.…

Shugaban Kasar Tanzaniya, John Magufuli ya yafe wa fursunoni sama da dubu biyar a bikin tunawa da cika shekara 58 da ’yancin kan kasar Tanzaniya.

A cikin wata sanarwar da ya gabatar a wajen bikin, Shugaba Magufuli ya ce za a saki wadansu daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci kan laifuffuka masu sauki yayin bikin ranar samun ’yancin kai ta kasar.

Magufuli ya kuma bayyana cewa wadansu mutane ba sa iya biyan tarar da aka yi musu, wadansu kuma na cikin wadanda suka aikata kananan laifuffuka kamar cin mutunci. Fursunoni dubu 35 da 800 ne ke tsare a  kasar kuma sama da rabinsu suna jira a yi musu shari’a ne.

Daga 1880 zuwa 1919, Tangayika na karkashin mallakar Jamusawa bayan ta kasance karkashin mulkin Ingila inda suka kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Kasar.

Bayan fafatawa na ƙungiyoyi neman ’yanci, Tangayika ta samu ’yancin kai a 1961, inda ta hadu da Zanzibar a 1963, wacce ta samu ’yancin daga Ingila a 1964, kuma tare suka zama kasar  Tanzaniya ta yanzu.