✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taraba: An kashe mutum 5 a sabon rikicin Tibi da Jukun -‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ta tabbatar da kashe mutum biyar a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun a Karamar…

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ta tabbatar da kashe mutum biyar a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun a Karamar hukumar Donga da ke jihar Taraba.

Kakakin runndunar ‘yan sandan jihar DSP David Misal, ya shaidawa majiyar mu hakan. Ya kuma ce a yanzu haka Mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan jihar na yankin don tabbatar da tsaro da samun zaman lafiya a garin.

Mataimakin Kwamshinan ne zai jagorancin rundunar ‘yan sandan da aka tura yankin.

Shugaban Kungiyar kabilar Tibi na jihar Mista Goodman Dahida, ya shaidawa majiyarmu cewa, ana zargin wasu matasan Jukun da kai hari kauyen Tse Akume inda suka kashe a kalla mutum 19.