✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tolulope: Kalli jana’izar mace ta farko mai tuka helkwaftan yaki

A ranar Alhamis 23 ga watan Yuli ake binne mace ta farko mai tuka jirgin sama na yaki a Najeriya, Tolulope Arotile. Ga wasu daga…

A ranar Alhamis 23 ga watan Yuli ake binne mace ta farko mai tuka jirgin sama na yaki a Najeriya, Tolulope Arotile.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda ake shirye-shiryen jana’izar da za a yi wa Tolutope a Makabartar Sojoji ya ke Abuja:


‘Yan uwan marigayiya Flying Tolulope Arotile a lokacin bikin jana’izarta a Makabartar Sojoji da ke Abuja.




‘Yan uwarta tare da limaman addinin Kirista a lokacin jana’izar a Abuja.
Hoto: Felix Onigbinde


Sojoji dauke da gawar Tolulope Arotile za su sanya ta a makwancinta.
Hoto: Felix Onigbinde

Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar yana mika tutar Najeriya ga ‘yar uwar mai rasuwar bayan an binne ta. Hoto: Felix Onigbinde



‘Yar uwar Tolupe a wurin jana’izarta.
Hoto: Felix Onigbinde


Bankwanan soji ga marigayiyar ta hanyar yin harbi sau 21 a makabartar sojoji, Abuja.  Hoto: Felix Onigbinde




Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olonisakin yana ajiye furen bankwana da karramawa a jana’izar Tolulope.
Hoto: Felix Onigbinde.