✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

TRUST TV ya zama Gwarzon Kafofin Yada Labarai na 2023

Trust TV ya lashe kambin ne a sakamakon rahotanninsa da binciken kwakwaf da kuma ilimantar da al'umma da yake yi a tsawon shekaru biyu da…

Gidan talabijin na Trust TV, mallakin kamfanin Media Trust, masu jaridar Aminiya da Daily Trust da Trust Radio ya lashe kyutar Gwarzon Kamfanin Yada labarai na 2023 na Majalisar Hazikai na Musamman (LEAA).

Trust TV ya lashe kambin ne a sakamakon rahotanninsa da binciken kwakwaf da kuma ilimantar da al’umma da yake yi a tsawon shekaru biyu da fara aikinsa.

A karrama gidan talabijin din da kambin ne a taron LEAA karo na uku da kamfanin Gaze Production ya karbi bakunci a Kaduna.

Shugaban LEAA, Adeyemi Adekunle, ya shida wa mahalarta cewa an shirya taron ne domin karrama mutane da kamfanoni da hukumomi da suka yi bajinta wajen kawo kyakkyawan sauyi a cikin al’umma.

Ya ce, “Na bibiyi shriye-shiryen Trust TV kuma na fahimci cewa kafar da labarai ce wadda babu kamarta idan aka kwatanta da sauran tashoshi, domin shirye-shiryensu sun dace da bangarori daban-daban na rayuwa.

“Shirye-shiryensu na siyasa da wasanni da na ilimantarwa suna matukar kayatarwa; Trust TV sun taka rawar gani kuma abin da muke yi a LEAA, shi ne mu zakulo hukumomi da ke yi abubuwan da suka dace mu karrama su.”

Da yake karbar kambin, Babban Jami’in kamfanin Media Trust mai kula da jihohin Kaduna da Kano, Ahmad Datti ya yi godiya ga masu shirya taron da suka ga dacewar Trust TV da kyautar Gwarzon Shekarar.