✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar abinci bala’i ne ga kasa

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin kasar nan da nufin hana shigo da shinkafa daga waje domin samar wa…

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin kasar nan da nufin hana shigo da shinkafa daga waje domin samar wa shinkafar da ake nomawa a Najeriya daraja.

Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hameed Ali (mai ritaya) ya bayyana cewa babu ranar bude kan iyakokin kasar, haka za a ci gaba da zama har sai mutanen kasar nan sun rungumi kayan abincin da ake nomawa a gida sun yi watsi da na kasashen waje.

Tunda aka rufe kan iyakokin  jami’an Kwastam suka himmatu wajen kama shinkafar da ake shigowa da ita, hasali ma dai har cikin kasuwanni suke bi suna kwace irin wannan shinkafa, wanda ya sanya a halin yanzu shinkafar ta fara wuyar samu, idan an samu kuma ana sayenta da tsada sosai.

Rahotanni sun nuna cewa a wasu wuraren ma ba a sayar wa mutum shinkafar waje sai an san shi, kuma da tsada za a sayar masa. Wannan ya sanya hatta shinkafar da ake samarwa a cikin gida ta fara tsada, domin kafin a dauki wannan mataki ana sayar da buhu daga Naira dubu 13 da 500 zuwa dubu 14 ne, amma yanzu farashinta ya doshi Naira dubu 18 ko ma fiye.

Ita ma shinkafar da talaka ke saye wadda ba a sanya a cikin buhu na burgewa ba, wato wadda ake aunawa, farashinta ya tashi, wadda ya sanya a halin yanzu shinfaka tana neman komawa sai dan sarki zai iya samu saboda tsadarta da kuma rashin kudin saye.

A cewar wani jigo a Kungiyar Manoma Shinkafa ta Kasa Malam Abba Dantata, ’ya’yan kungiyarsu har yanzu ba su sayar da buhun shinkafa fiye da Naira dubu 14, wadansu ma har a Naira dubu 13 da 500 ko Naira dubu 13 da 800 ko da 900 suke sayarwa,  ’yan kasuwa ne kawai suke tsawwala farashin shinkafar.

Hakika tsadar abinci ba alheri ba ne ga kasa, domin noma ba dole ba ne ga kowa, amma cin abinci dole ne ga kowa. Domin haka hakkin gwamnati ne ta tabbatar mutanen kasarta sun samu abincin da za su ci wadatacce kuma a farashi mai sauki, shi ya sanya a Jamhuriya ta Daya gwamnati ta kafa Hukumar Sayen Kayayyakin Gona da nufin taimaka wa manoma wajen sayar da amfanin gonarsu da daraja, inda gwamnati za ta sayi amfanin gona komai yawansa ta adana shi a rumbuna tana sayar wa jama’a a farashi mai rangwame. Wato gwamnati ta taimaka wa manoma wajen sayen amfanin gonarsu da daraja domin karfafa musu gwiwa su ci gaba da noma, ta kuma taimaka wa masu saye su ci ta hanyar sayar musu da abincin a farashi mai rahusa. Hakan ya sanya kowa yana farin ciki, da manoma da masu saye su ci.

Amma a halin yanzu ga dukkan alamu gwamnati ba ta damu da masu sayen abincin su ci ba, ta fi sha’awar taimaka wa manoma domin su sayar da amfanin gonarsu da daraja, saboda a ganinta ta haka ne za a jawo ra’ayin mutane su rungumi sana’ar noma.

Ya kamata gwamnati ta fahimci cewa masu cin abinci sun fi masu noma yawa kuma ba zai yiwu kowa ya koma gona ba, domin a halin yanzu hamshakan masu kudi ne suke da manyan gonaki da suka saya a wurin talakawa kuma mafi yawan gonakin da talakawa ke nomawa yanzu sun zama gidajen jama’a saboda kusancinsu da cikin gari.

Yanzu idan manomi zai yi noma sai ya shiga mota ko ya hau babur ya yi tafiya mai nisa kafin ya isa gonarsa, sabanin a baya da zai taka da kafarsa tare da yaransa su tafi gona ba tare da ya kashe ko kwabo ba.

Yanzu noma sai da kudi, domin ana bukatar kudin shiga mota zuwa gonar da kudin biyan leburori da kudin sayen taki da maganin kwari da dai sauransu. Kuma a halin da ake ciki na matsatsin rayuwa mutane da dama suna son yin noman amma ba su da kudin daukar dawainiyar noman.

Haka kuma matsalar tsaro ta hana manoma yin noma, domin kiri-kiri ana ji ana gani ’yan ta’adda sun hana mutane da dama zuwa gonakinsu. Idan manoma suka yi karfin hali suka tafi sai a kama a yi garkuwa da su sai sun biya kudin fansa, a wani lokacin ma kashe su ake yi, kamar yadda aka yi a wani yanki a Jihar Katsina inda ’yan ta’adda suka kashe manoma a gonakinsu saboda wai sun ki jin gargadin da suka yi musu na cewa kada wanda ya yi noma a wannan shekarar.

Saboda haka ya kamata shugabanni su bude kunnuwansu kuma su rika bincikar duk wani rahoto da ake ba su, domin gaskiyar magana mafi yawan rahotanni da fadawansu suke kai musu suna tattare da fadanci ne kawai, domin ba su fada wa shugabannin irin mawuyacin halin da talakawa ke ciki.

Wadanda gwamnati ke tattaunawa da su ba kananan manoma ba ne, hamshakan manoma ne, kuma su ne suke cin moriyar tsauraran matakan da gwamnati take dauka, domin su ne suke noma mai yawa da za su ci kuma su sayar har tsawon shekara guda ko fiye, amma karamin manomi ko abincin da zai ci a shekara bai iya nomawa saboda rashin karfin aljihu, saboda a cikin dan abin da ya noma ne zai diba ya sayar ya biya bukatunsa, sauran kuma ya ajiye don ya ci, kuma bayan lokaci kankane abincin nasa zai kare ya koma yana awo, wato shi ma ya shigo layin masu ci ke nan.

Saboda haka murnar da wadansu suke yi saboda farashin abinci yana tashi murnar banza ce, domin matsalar za ta zagayo ta shafe su ko wani nasu.

Wajibi ne gwamnati ta tabbatar al’ummarta suna samun abinci wadatacce kuma a cikin sauki, ta haka ne za a samu nagartacciyar al’umma mai cike da koshin lafiya, domin yunwa makunshin cuta ne, saboda mafi yawan cututtuka daga rashin abinci masu gina jiki ake samunsu.

Marigayi Faisal Sarkin Saudiyya, ya taba bayyana cewa yana alfahari da cewa a zamaninsa abincin da sarki zai ci a gidansa shi ne talaka zai ci a nasa gidan, saboda an saukaka komai na abinci da kayan marmari yadda kowa zai iya samu. Amma idan ya kasance shugabanni suna cin kaji talakawansu kuma suna cin kofato lallai akwai matsala.