✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsare Al-Mustapha shekara 15 rashin adalci ne – Al-Makura

Gwamnann Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bayyana tsare tsohon dogarain Shugaba Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha na tsawon shekars 15 a gidan kaso a…

Daga hagu Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ne yake karrama Manjo Hamza Al-Mustapha lokacin da ya ziyarci jihar a makon jiyaGwamnann Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bayyana tsare tsohon dogarain Shugaba Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha na tsawon shekars 15 a gidan kaso a matsayin rashin adalci, inda ya ce saboda lura irin wannan dalili da wasu dalilai gwamnatinsa ta fara aiwatar da sauye-sauye ga dokoki a jihar.
Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabin maraba da Manjo Al-Mustapha a masaukin baki na Shugaban kasa bayan da Al-Mustapha ya ziyarci jihar a karshen makon jiya.
Gwamna Tanko Al-Makura ya nanata kudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci da walwala ga jama’a, inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi dokoki domin tabbatar da ana gudanar da shari’o’i akan lokaci kuma cikin adalci.
Gwamna Al-Makura ya bukaci Manjo Al-Mustapha ya yafe wa wadanda suka kulla masa sharri, a cewarsa haka Allah Yake bukata.
Sai ya yaba wa hangen nesan marigayi Janar Sani Abacha wajen kirkiro Jihar Nasarawa a 1996 inda ya ce ba shakka Janar Abacha ya kafa tarihi kuma al’ummar jihar ba za su manta da shi ba a rayuwansu.
Tun farko Manjo Al-Mustapha wanda ya samu rakiyar matarsa da Mohammed Abacha da wasu magoya bayansa ya ce ya ziyarci jihar ne musamman Lafiya domin mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya da shugabannnin addini da al’ummar jihar da suka jajanta masa lokacin da yake fuskantar shari’a.
Ya ce Jihar Nasarawa tamkar jiharsa ce saboda haka ya zame masa wajibi ya kawo wannan ziyara bayan shekaru da dama da ya yi a gidan kaso.
Ya yaba wa Gwamna Al-Makura kan nasarori da ya cimma a shekara biyu kacal, inda ya bukace shi ya ci gaba da yin haka.
Manjo Al-Mustapha ya ziyarci fadar Sarkin Lafiya Dokta Isah Mustapha Agwai inda Sarkin ya bukace shi da kada ya dauki fansa, kuma ya yafe wa wadanda suka nuna masa rashin adalci.