✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsintar gawarwakin almajirai biyar a Jigawa ta haifar da rudani

Al’ummar garin Gwaram da ke karamar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa sun wayi gari cikin rudani sakamakon tsintar gawarwakin wasu almajirai biyar da aka yi…

Alhaji Sule Lamido, Gwamnan Jihar JigawaAl’ummar garin Gwaram da ke karamar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa sun wayi gari cikin rudani sakamakon tsintar gawarwakin wasu almajirai biyar da aka yi yashe a kan titi kusa da wani gida.
Wannan lamari ya sa ’yan sandan yankin sun kai samame inda suka kame wasu makwabtan wurin su uku da ’yan sandan suka ki fadin sunayensu kuma ba su fadi dalilin yin hakan ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ASP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda aka samu gawarwakin nasu akwai ayar tambaya a kan mutuwarsu wadanda dukkansu samari ne masu kananan shekaru.
An bayyana sunayen marigayan da Basiru M. Inusa mai shekara 12 da Mansur Inusa mai shekara 12 da Rabi’u Abubakar mai shekara 10 da Bashir Yunusa mai shekara 13 kamar yadda ASP Abdu Jinjiri ya tabbatar. Ya ce dukkansu almajirai ne kuma tuni aka kai gawarwakinsu zuwa Asibitin Malam Aminu Kano domin a gudanar da bincike don gano abin da ya yi sanadin rasuwar almajiran biyar a lokaci daya.
Ya ce yanzu haka sun damke wasu mutum uku makwabtan wurin da aka samu gawarwakin almajiran biyar su uku suna hannun jami’an tsaro suna amsa tambayoyi a kan musabbabin mutuwar yaran, kuma da zarar sun kammala bincike za su sanar da manema labarai hakikanin gaskiyar lamarin.
Wasu jama’a da suka bukaci a sakaya sunansu daga yankin na Gwaram sun shaida wa wakilinmu ta wayar cewa ana zargin wasu ’yan siyasa ne da aikata miyagun ayyuka da wasu sassa na jikin dan Adam yayin da wasu suke cewa wai watakila wani ne ya ba yaran abinci mai guba a ciki suka ci a lokacin azumi.
Sai dai ASP Jinjiri ya musanta cewa matsafa ne suka yi aika-aikar, domin babu wata alama da ta nuna a yanka ko an ciri wani sashi na jikin yaran. “Amma tun da an kai gawar yaran wurin
likitoci don yin binchike a gano ko abin da ya yi
sandin mutuwarsu a jira a ji abin da binciken zai nuna,” inji shi.