✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsintuwa

Wadansu Kanawa ne suka je Kudu neman kudi, suna cikin tafiya sai suka tsinci jikkar kudi makare da dukiya. Nan da nan suka tari mota…

Wadansu Kanawa ne suka je Kudu neman kudi, suna cikin tafiya sai suka tsinci jikkar kudi makare da dukiya. Nan da nan suka tari mota suka shiga, suna hira, suna bayanin yadda za su kashe kudin. Ashe direban yana jin Hausa, don haka ya fahimci duk abin da suke ciki. Yana tsakar tafiya sai ya kashe motar da gangan, ya ce masu su sauka su tura. Suka sauka suna tura mota, alhali jikkar kudin da suka tsinta tana cikin but din mota. Ya tada mota, ya fizge ta, ya bar su galala.

Daga Nusa Aminu Manaja, Sakkwato 07068681050