✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon soja

Wani tsohon soja ne mura ta dame shi sai ya je wajen mai kemis domin sayen magani. Da ya je sai mai kantin ya ce:…

Wani tsohon soja ne mura ta dame shi sai ya je wajen mai kemis domin sayen magani. Da ya je sai mai kantin ya ce: “Ba ni da maganin mura, ya kare sai Loko. Shi kuma yana da zafi.” Sai tsohon sojan nan ya ce: “Yaro, lokacin yakin duniya na biyu sai da tiyagas ya zama ruwan sha na.” Sai mai kemis ya ba shi Loko, dayake shi kuma Naira dari ya ba shi, sai ya ce bari ya je ya nemo canji. Kafin ya dawo daga neman canji, soja ya lakaci Loko ya sa a hancinsa. Mai kemis ya dawo ya tarar da shi yana ta fareti a kan hanya, kowa ya gani sai ya tambaye shi cewa: “Malam, wai don Allah hancina yana nan bai cire ba?” Sai a ce masa yana nan
Daga A.D. China, 08034463170