✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tsoron Allah na da tasiri ga shugaba’

Babban Sakataren Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Ishak Oloyede ya bayyana bukatar da ke akwai ga ’yan siyasa da su cika…

Babban Sakataren Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Ishak Oloyede ya bayyana bukatar da ke akwai ga ’yan siyasa da su cika alkawuran da suka dauka, a lokutan yakin neman zabe.

Farfesa Oloyede wanda ya fadi hakan ne ta bakin Ustaz Idris, wanda shi ne shugaba na farko na Majalisar Musulmi ta Abuja, a wajen taron kara wa juna sani na watan Ramadan karo na 13 da Kungiyar ’Yan Jarida Musulmi reshen Abuja suka shirya a Abuja.

“Shugabanci wani irin aiki ne mai hadarin gaske. Mutane na daukar alkawura, ba tare da tunanin yadda za su cika alkawuran ba. Nan gaba za a nemi ka yi bayanin alkawuran da ka dauka, imma a nan duniya ko kuma gobe kiyama. Don haka, yana da muhimmaci mu zama masu cika alkawuran da muke yi.”

Ya yi kiran da ana matukar lura tare da yin taka-tsantsan wajen zabar wadanda za su shugabanci al’umma, inda ya ce tsoron Allah na tasirin gaske ga nagartan shugabanni. Ya kuma jinjina wa kungiyar wajen fitar da muryar musulunci.

Babban Bako mai jawabi a wajen, mai wa’azi na kungiyar Ansar-Ud-Deen, Dokta Musa Olaofe wanda ya yi jawabi mai taken “Cika alkawuran zabe” ya ce lallai ne musulmi su zama masu tsoron Allah a wajen gudanar da mulki koda yaushe.

Oloefe ya kuma bukaci dukkan shugabanni da su zama masu amana tare da bitar alkawuran da suka daukar wa masu zabe.