✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ubangiji daga farko (1)

“Muhimmin abu na farko, sai ku kwallafa rai ga al’amuran mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a kara muku dukan wadannan abubuwa” Matiyu…

“Muhimmin abu na farko, sai ku kwallafa rai ga al’amuran mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a kara muku dukan wadannan abubuwa” Matiyu 6:33

Barkanmu da sake haduwa a wannan mako. Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa da alheranSa zuwa gare mu. Za mu yi nazarinmu a kan sanya Ubangiji daga farko a cikin komai. Abin da ya fi muhimmanci a rayuwar dan Adam shi ne Ubangiji Mahalicinsa, domin Shi ne farko da kuma karshen komai da kowa, Shi kadai Ya san abin da zai faru yanzu da nan gaba da kuma har abada cikin rayuwar dan Adam. Da sanin haka sai mu sa zuciya mu girmama Ubangiji Allah a koyaushe cikin rayuwarmu, domin mu ci moriyar albarkarSa mai yawa. Akwai abubuwa da dama da ba mu da sanin cewa albarka ne sai idan muka sanya Ubangiji a farko cikin rayuwarmu da harkokinmu na yau da kullum. Misali, za ka ga wani dan kasuwa ko ma’iakaci da yake da kwazo a cikin harkokinsa amma ba ya da kwanciyar hankali, musamman lokacin da harkokin ba su tafiya yadda ya zata ko ya shirya wa kansa. Wani lokaci har wadansu sukan sa kansu a cikin halin rashin lafiya ko hauka ko kisan kai, me ke kawo irin wannan yanayi? Rashin sanin Ubangiji da kuma albarkar da ke cikin sanya Shi a farko cikin komai. Domin damka komai cikin hannun Ubangiji da farko kan ba da kariya da riba da albarka. (Karin Magana 16:3) Ka roki Ubangiji, Ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su. Ka roki Ubangiji a kan harkokinka na yau? Gama mun ji, mun gani, mun kuma shaida abubuwan da Ubangiji yake yi cikin rayuwar mai bi na gaskiya. Rashin sanya Ubangiji a cikin harkoki da rayuwar dan Adam alama ce da ke nuna kaunar da muke da ita ga kayan duniya ta wurin ikon kanmu, hatta nuna kauna ga dan uwanka ma zai yi wuya, Yesu Almasihu ya ce, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan karfinka da dukan hankalinka. Ka kuma kaunaci dan uwanka kamar kanka.” (Luka 10:27).  

Mu sani fa cewa idan Ubangiji ba Ya cikin harkokinmu na yau da kullum babu shakka mun gayyaci Shaidan ke nan. Shi ya sa za ka ga mutane da dama suna fama da rashin lafiya (Domin kwadayin kayan duniya), wadansu ma na tunanin kisan kai (da talaka da mai dukiya) da dai sauransu. Wadannan halaye kuwa ba daga wurin Ubangiji ba ne domin Ubangiji ba zai taba sanya ka ka yi kisan kai ba, ba zai kuma sanya ka kwadayin kayan duniya ba, domin irin wadannan halaye sun saba wa maganarSa, gama maganarSa tana cewa, “Kada ku kaunaci duniya, ko abin da yake a cikinta. Kowa ke kaunar duniya, ba ya kaunar Uba ke nan sam. Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha’awa irin ta halin mutuntaka da sha’awar ido da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne. Duniyar kuwa tana shudewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dauwama har abada.” (1 Yahaya 2:15-17). 

Abin da Ubangiji ke bukata a gare mu shi ne, mu kaunace Shi da dukan ranmu, (Kolosiyawa 3:1-4), “To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah. Ku kwallafa ranku a kan abubuwan da suke sama, ba a kan abubuwan da suke a kasa ba. Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah.” Haka kuma kaunarSa kuwa sai mu bide shi da farko cikin kowane irin hali, idan kuma rashin biyan bukata ne ke hana ka bidar Ubangiji da farko cikin harkokinka da rayuwarka, ka ji abin da maganar Allah ke fadi cikin Littafin Matiyu 6:31-33 “Don haka kada ku damu, cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sanya?’ Ai, al’ummai ma suna ta neman duk irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka. Muhimmin abu na farko, sai ku kwallafa rai ga al’amuran mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a kara muku dukan wadannan abubuwa.”

To, idan har Ubangiji Yana sane da bukatunmu, me zai hana mu neman fuskarSa da farko cikin rayuwarmu? Mu fito daga cikin halin rashin sani, mu nemi fuskar Ubangiji domin mu mori albarkar da ke kunshe cikin zumunci da Shi. 

Sai mu zauna da sanin cewa “Ai daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. daukaka ta tabbata a gare Shi har abada. Amin.” (Romawa 6:36).

Bari mu sanya Ubangiji Allah da farko a cikin komai a wannan sabuwar shekara, mu sabunta rayuwarmu, mu nemi nufinSa cikin komai a koyaushe, mu zama masu binciken LittafinSa Mai tsarki, masu addu’a kuma a koyaushe kamar yadda Ya umurce mu mu yi, ta wurin yin haka ne za mu yi kusa da Shi, Shi kuma Ya kasance tare da mu. 

Shalom.