✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ukasha: Bahaushen da ya zamo Ibo bayan shekara 8 a hannun wadanda suka sace shi

Ranar Juma’ar da ta gabata, rana ce da za a iya cewa rana ta biyu da aka sake haihuwar wani yaro mai suna Ukashatu Rogogo.…

Ranar Juma’ar da ta gabata, rana ce da za a iya cewa rana ta biyu da aka sake haihuwar wani yaro mai suna Ukashatu Rogogo.

Rana ce da Ukashatu ya sake tsinto asalinsa bayan ya rasa shi shekara takwas da suka gabata. Ukashatu mai shekara 14 a duniya ya rasa asalinsa na Bahasuhe da aka haifa a kauyen Rogogo da ke Karamar Hukumar Baure a Masarautar Daura da ke Jihar Katsina ce bayan da wata mace ’yar kabilar Ibo ta sace shi a Legas lokacin da mahaifiyarsa mai suna Daharatu ta tafi da shi yawon bara a can shekara takwas da suka gabata.

Ukashatau mai shekara 6 a lokacin da aka sace shi, wadanda suka sace shi sun canja masa suna zuwa Michael kuma suka nuna wa makwabta cewa dansu ne na cikinsu, inda a cikin wadannan shekaru ya rasa harshensa na Hausa ya koma yana magana da harshen Ibo, kafin a kubutar da shi a ranar Juma’ar makon jiya.

Bayan fara jin labarinsa a sashin Hausa na BBC, Aminiya ta yi tattaki zuwa kauyensu na Rogogo inda ta iske ba ya jin Hausa kwata-kwata, sai Ingilishi (Pidgin) da kuma harshen Ibo.

Da yake amsa tambayoyin wakilinmu cikin Ingilishin Pidgin kan yadda aka yi ya bace, Ukashatu ya ce, “Na fita zan zubar da shara ce a layin da muke a Legas, sai wata mata ta kira ni cewa in zo in karbi burodi. Bayan ta ba ni burodin, sai ta ce in zo mu je ta ba ni shinkafa. Sai na bi ta har muka shiga wani gida. Daga nan muka fito muka sake shiga wani gidan. To tunda muka fito daga wancan gida, ban sake sanin inda nake ba.”

Xahara da Ukashatu da yayansa Qasimu Abdu

Ukashatu ya kara da cewa: “Matar mai suna Christiana Onechukwu da mijinta Matthew, suna da ’ya’ya biyu masu suna Emmanual da Ifeanyi. Sai ni da suka canja wa suna zuwa Michael, sai kuma wata yarinya Bayarbiya wadda suka kawo daga baya.”

Ukashatu ya ce, wadannan sababbin iyaye nasa ’yan kabilar Ibo sun ce shi ma Ibo ne, kuma su ne iyayensa. Sai dai ya ce ba zai iya gane yadda aka yi ya rasa harshensa na asali na Hausa ba, kawai ya iske kansa ne ba ya iya magana da shi. “Sun sanya ni a makarantar firamare ta Goody, kuma a yanzu ina aji biyu ne a Karamar Sakandare ta Morocco. Suna ba ni abinci da tufafi, suna kula da ni sosai,” inji shi.

Ukashatu wanda ya saba rayuwa a wajen wani masallaci a matsayinsa na yaro Musulmi, su Matthew sun canja masa addini zuwa addinin Kirista. Ya ce da shi ake zuwa coci wajen ibada duk kuwa da cewa har zuwa wannan hira da yake yi da Aminiya bai san abin da ake yi a cocin ba balle ya fahimta.

Game da yadda aka yi ya kubuta daga hannun mutanen ya ce, “Waccan yarinya Bayarbiya ita ce ta gudu saboda ana ba ta wahala. Ta ce mini za ta gudu amma in yi shiru kada in fadi. Ta gudu ta je ta yi rahoto ga ’yan sanda aka zo aka tafi da mu. Ban san yadda aka yi na tuna da mahaifiyata ba lokacin da ’yan sandan suke tambayata. Na gaya musu cewa, mahaifiyata ba ta gani, na kuma fadi inda take, sai muka je wajen, a karshe da na ganta na gane mahaifiyata.”

Yaya batun karatu da kuma rashin jin harshen Hausa alhali ga shi an maido shi kauyensa na asali?

Sai Ukashatu ya ce, a yanzu yana jin dadi domin yana tare da yara ’yan uwansa. Kuma ya sani a hankali zai koma ya ji Hausar tunda ita ce ta haife shi, kuma ya san yana yin ta da farko, amma bai san yadda aka yi ya bari ba. Karatu kuma zai ci gaba.

Mahaifiyar Ukashatu mai suna Daharatu makauniya ce mai kimanin shekara 50 kuma ta rasa kafa daya sakamakon hadarin mota da ta samu sanadin zuwa Legas yawon bara, ita ce ta tafi da shi Legas din, inda aka sace shi ya shafe shekara takwas ba tare da sanin inda yake ba, ballantana halin da yake ciki.

Malama Dahara ta shaida wa wakilinmu a kauyen Rogogo yadda ta rasa Ukashatu wanda shi ne danta na shida daga cikin ’ya’yanta tara tun yana da shekara 6, sai bayan da ya cika shekara 14 Allah Ya dawo mata da shi.

Dahara ta ce, “Wata ranar Alhamis ce da misalin karfe takwas na dare a bakin Masallacin Oyuye da ke Legas na aike shi ya zubar da sharar da muka tattara. Tun daga waccan rana ban sake ganinsa ba, sai fa Juma’ar da ta wuce. Ita sharar muna tattarawa ne a kai can wajen wani turken lantarki idan gari ya waye sai mu ba masu kwasar shara dan wani su kwashe, domin a nan ne muke zaman bara.”

Dahara ta shaida wa Aminiya cewa tana zuwa da Ukashatu garin Legas ne don yin bara, inda ta ce a can ma ne ta yi rainon cikinsa bayan ta samu daga gidan mijinta. “Dalilin zuwana can shi ne, ina zuwa yawon bara saboda nakasar da nake da ita. To bayan tura shi zubar da shara, shiru-shiru bai dawo ba, nan muka shiga nemansa ni da abokan arziki da muke zaune tare. Mun je asibitoci da ofisoshin ’yan sanda bakin gwargwado, amma shiru babu labarinsa, sai wannan rana ta Juma’a,” inji ta.

Game da yadda aka yi suka sake haduwa da dan nata bayan tsawon wancan lokaci, sai ta ce, “Ina cikin masallacin Maryland a ranar Juma’a, bayan an gama Sallah da karfe daya da rabi, sai muka je inda ake yin ta karfe biyu inda a nan ne muke yin barar, sai aka kira ni daga gidan da muke zaune. Mai yi mani jagora mai suna Dankuri ne ya dauki wayar, sai aka ce masa ya gaya mini ga Ukashatu nan an kawo. Ai daga nan babu batun bara sai gida. Lokacin da na je gidan ban same shi ba, sai aka ce yana ofishin ’yan sanda na Oyibo, sai muka tafi ni da wani mai suna Tasi’u. Bayan mun shiga muka ce mun zo ne a kan maganar yaron da aka kai Kubaba. A nan ne suka fito da shi, har ya nufo inda nake, sai suka tsayar da shi suka ce ya koma baya. Har ila yau suka sake ce masa ya taho. To a nan suka ce mu je can wurin babbar ma’aikatar tasu. A karshe dai da aka sake turo shi wurina da zuwansa sai kawai ya rungume ni, ni da shi sai kuka yana share mini hawayen da ke fitowa.”

Malama Dahara ta ci gaba da cewa, jami’an sun gaya mata yadda aka yi har suka gano Ukashatu ta hanyar wata yarinya da ta kawo koke a wajensu dangane da wadda suke hannunta.  “Gida daya suke da Ukasha wanda take kira da sunan Malam, saboda ta ce shi ba dan kabilar Ibo ba ne kamar yadda iyayen karyar suka shaida masa. An ce yarinyar Bayarbiya ce, ita ce ta kawo rahoto ga ’yan sandan saboda gajiya da ta yi kan irin azabtar da ita da suke yi a zaman shekara biyar da ta yi da su. Domin Ukasha na da shekara uku a hannunsu suka kawo ta. Ga yadda ake ba ni labari an ce,an turo ta zuwa makaranta wannan mata mai suna Christiana ta hadu da ita a hanya kawai sai ta dauke ta ta sanya a mota ta yi gaba da ita. To wancan matsi da ta sha, ya sa ta samu wata damar da ta fito ta kai rahoto ga ’yan sanda suka bi suka kamo waccan mata da mijinta. To bayan sun kamo su ne suka tambayi Ukashatu inda yake ya shaida musu, shi ne suka kawo shi nan Kubaba inda muke zaune,” inji ta.

Sai dai batun gane mahaifiyarsa bai zamo abu mai wuya ba ne ga Ukashatu saboda ya kai shekara 6 kafin a sace shi.

A lokacin da ’yan sandan ke kokarin tantance lamarin wannan yaro, sai da ya amsa musu duk wata tambayar da suka yi gami da kai su duk wasu wuraren da ya san suna zuwa yawon bara da mahaifiyarsa kafin su hadu da ita.

Dahara ta ce, ba ta san yadda aka kwashe da waccan mata wadda ta raba ta da danta ba na tsawon lokaci, ta bar ta a can hannun hukuma bayan tabbatar da aiwatar da wancan mummunan aiki gare su. Kuma bayan an ba ta danta ne suka taho gida.

Wani abin da ya ba Aminiya mamaki shi shi ne yadda Dahara ta ce ba za ta bar zuwa yawon bara a Legas ba, bisa hujjar cewa bara a can ta fi nan Arewa, kuma ta saba yin bara a can.

Ta ce abin da kawai ta bari shi ne, tafiya da yara, A cewarta kanwar Ukashatu wadda ta haifa da wani mijin kuma wadda tana goyonta aka sace shi, ta mayar wa dangin mahaifin yarinyar saboda rasuwar mahaifinta.

Wadansu na kusa da Daharatu sun shaida wa Aminiya cewa ta yi sama da shekara 20 tana zuwa bara a Lagas. Sai dai ta dawo gida ta yi mako daya ko ’yan kwanaki ta koma kuma sai an gan ta. “Hatta wannan kafa daya da ba ta da ita wadda aka yanke sanadiyyar wani hadari  da aka yi da ita a hanyar Legas, mun yi zaton za ta bar zuwa, amma da warkewarta ta koma,” inji wani da ya nemi a sakaya sunansa.

Malam Kasimu Abdu daya daga cikin yayyen Ukashatu, ya ce ba karamin dadi suka ji ba na sake haduwa da dan uwansu wanda a da suka fitar da rai.

Ya ce tun lokacin da suka samu labarin bacewarsa suka shiga yin addu’a, ba su kuma daina ba har lokacin da Allah Ya maido musu shi.

Aminiya ta so jin ta bakin mahaifinsa amma hakarta ba ta cimma ruwa ba saboda mahaifin ba a garin Rogogo da ke yake ba.