✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa’adi na biyu: Gwamnan Kogi ya kori mataimakansa

Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello, ya kori mataimakansa bayan mako biyu da sake dawo wa wa’adi na biyu a matsayin zababben Gwamnan jihar Kogi.…

Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello, ya kori mataimakansa bayan mako biyu da sake dawo wa wa’adi na biyu a matsayin zababben Gwamnan jihar Kogi.

A cikin wadanda ya kora akwai mataimaka na musamman da manyan mataimakansa na musamman da sauran wasu masu yi masa hidima.

Sakatariyar Gwamnatin jiharv Dakta (Misis) Ayoade Folashade Arike,  ce ta fitar da sanarwar a yau Litinin, ta kara da cewa duk wadanda korar ta shafa su mika takardunsu ga manyan ma’aikan da suke da hukumomin da suke aiki.