✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu mutane na daukar lambobin katin zabe a kauyukan Taraba

Wasu mutane maza da mata sun shiga kauyukan Jihar Taraba suna bin gidaje suna daukar lambobin katunan zabe.Mutanen karmar yadda binciken wakilinmu ya gano sun…

Wasu mutane maza da mata sun shiga kauyukan Jihar Taraba suna bin gidaje suna daukar lambobin katunan zabe.
Mutanen karmar yadda binciken wakilinmu ya gano sun shiga wasu sassa na kananan hukumomin Gassol da Bali da Karin Lamido da Jalingo.
A garin Sabon Gida da ke karamar Hukumar Gassol wasu mata sun shiga gidajen matan aure inda suka ce wai Hukumar Zabe ta kasa (INEC) a jihar ce ta sa su wannan aiki.
Wani magidanci a Sabon Gida mai suna Malam dantsoho Garba ya shaida wa wakilinmu cewa mata biyu sun shiga gidansa a lokacin da ba ya nan suka karbi katunan zabensu suka dauki lambobi da ke ciki.
Malam dantsoho ya ce bayan ya dawo gida ne iyalinsa suka fada masa abin da ya faru, kuma da jin haka sai ya shaida wa ’yan uwansa suka shiga lunguna don nemo mutanen. “Mun yi nasarar samun wasu mata biyu dauke da takardu a hannunsu, wadanda suka kasa ba mu kwakkwarar amsa kan dalilin da daukar lambobin katin zaben, sai muka kwace takardun muka umarci matan su bar garin a cikin gaggawa,” inji shi.
Bincikenmu ya gano an samu irin haka a wasu unguwanni da ke cikin garin Jalingo, kuma an shaioda wa wakilinmu cewa a wasu lokuta mutanen suna yin alkawarin bayar da kudi masu yawa in za a yarda su tafi da katin zaben.
Kakakin Hukumar INEC a jihar, Mista Fabian bwamhi ya shaida wa wakilinmu cewa sun samu wannan labara, kuma hukumarsu ba ta tura kowa ya dauki lambar katin zabe ba. Ya shawarci jama’a su kai rahoton duk wanda ya nemi daukar lambar katin zabensu ko ya nemi sayen katin zaben.