✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

West Ham tana zawarcin Moses

Kulob din West Ham United da ke Ingila a ranar Talatar da ta gabata ne ya ce yana yunkurin dauke dan kwallon Chelsea na Ingila…

Kulob din West Ham United da ke Ingila a ranar Talatar da ta gabata ne ya ce yana yunkurin dauke dan kwallon Chelsea na Ingila kuma haifaffen Najeriya bictor Moses kafin a rufe kakar saye da kuma sayar da ’yan kwallo.&nbsp Kulob din ya ce tuni ya shiga tattaunawa da kulob din na Chelsea akan yiwuwar dauke dan kwallon. Rahotaon da kafar sadarwar Daily Telegraph ta kalato ya ce ana ganin kulob din zai dauke Moses ne bayan ya taya shi a kan Fam miliyan 7 cinikin da ake ganin da wuya kulob din Chelsea ya kawar da kai. Chelsea ta yi niyyar sayar da Moses ne bayan ta samu nasarar ccefano Pedro daga FC Barcelona na Sifen.