✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wizkid ba tsarana ba ne – mawaki Dabido

Mawakin nan da tauraruwarsa ke haskawa a halin yanzu, ‘OBO’ (Omo Baba Olowo) wato Dabido, ya fito karara ya musanta labarin da ya karade gari…

Mawakin nan da tauraruwarsa ke haskawa a halin yanzu, ‘OBO’ (Omo Baba Olowo) wato Dabido, ya fito karara ya musanta labarin da ya karade gari cewa yana gasa ne da abokin sana’arsa Ayo Balogun, wanda aka fi sani da lakanin Wizkid.

Dabido, wanda asalin sunansa Dabid Adeleke ya ce shi ba ya gasa da kowa, domin kuwa sha’anin gabansa kawai yake yi, a yayin da shi ma Wizkid ke nasa sha’anin.
A wata tattaunawa da ya yi da ’yan jarida kwanan nan, Dabido ya ce: “Ba na yin gasa da Wizkid ta kowane hali. Wananna jita-jita da ake yadawa ba ta dame ni ba kuma ni ba na kallon wani mawaki da zan ce zan yi gasa da shi, ko kuma a ce wai zai iya kawo mani cikas. Allah yana tare da ni, don haka nakan shiga situdiyo ne kawai in buga wakata kuma komai yana tafiya yadda ya kamata.”
Ya kara da cewa: “Ni da kaina nake kirkirar wakokina sannan kuma na rubuta su a sutidiyo. Ba na tsoron gasa da kowa kuma ba na tsoron cewa wai wani zai hada kafada da ni sannan ya doke ni wajen farin jini ko amsuwa ga jama’a. Ni dai na san kowa da lokacinsa, domin mutum ba zai dawwama yana tashe ba. Amma da zarar kana da inganci, za ka yi waka mai inganci kuma za ka samu masoya da yawa. Wannan shi ne kawai abin da ake bukata.”
Dabido dai ya samu daukaka ne a sakamakon wakarsa ta ‘Skelewu’ wacce a yanzu haka take cin kasuwarta ga matasa. Mutane na kokarin kwatanta shi da matashin mawaki Wizkid, ko wa za a ce ya fi dayan shahara da daukaka?