✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya rasu lokacin da yake dinka kayan Sallah

Da yammacin ranar jajibarin karamar Sallah al’umar garin Agege a Legas suka samu kansu cikin alhinin rashin wani matashi mai sana’ar dinki wanda Allah Ya…

Da yammacin ranar jajibarin karamar Sallah al’umar garin Agege a Legas suka samu kansu cikin alhinin rashin wani matashi mai sana’ar dinki wanda Allah Ya karbi ransa yana tsaka da dinkin kayan Sallah wanda abokan huldar shi su ka ba shi domin ya dinka masu su yi hawan Sallah.

Marigayin mai suna Muhammad Auwal da ke zaune a unguwar Gwagwalo ya rasu yana da shekaru 26 bayan da ya fita daga cikin hayyacin sa a lokacin da yake tsaka da dinkin kayan Sallah a kuma yi an jana’izar sa da sanyin safiyar yau Sallah da misalin karfe 8 na safe, ya rasu ya bar ‘yan uwa da abokan arziki.

Muna fatan Allah Ya jiqan sa ya yi masa rahama