✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakamata a bar ’yan Najeriya da ke kasashen waje su yi zabe, ko a’a?

A kwanakin baya ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa tana duba yiwuwar bai wa ’yan Najeriya da ke zaune a kasashen ketare…

A kwanakin baya ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa tana duba yiwuwar bai wa ’yan Najeriya da ke zaune a kasashen ketare damar kada kuri’arsu lokacin zabe daga can. Abin tambaya nan shi ne, shin daukar wannan matakin ya dace? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

 

Matakin ya dace – Alhaji Isyaka Hadeja

Daga Musa Kutama, a Kalaba

Alhaji Isyaka Hadeja; “Hakan yana da kyau, ya dace a bar su su yi zabe ai suma ’yan Najeriya ne kuma Allah ne Ya yi zaman su a can. Idan aka yi musu haka an yi adalci musamman ma yanzu da aka zama duniya ta dunkule ta hanyar fasahar nan ta zamani wato Intanet. Ba sai ansha wahalar daukar akwatin zabe daga wata kasa zuwa wata ba domin wannan ma wata hanyace ta kashe kudi.”

Matakin ya yi daidai  – Alhaji Khamis

Daga Musa Kutama, a Kalaba

Alhaji Khamis Mai Adashi: “Ya kamata a bar su su kada kuri’a saboda suma suna da ’yanci ai ’yan kasa ne, idan kuma ka duba ai sauran kasashen waje  ma da suka ci gaba ai suna bari ’yan kasarsu su jefa kuri’a a inda suke da zama.Bama wadanda ke a nahiyar Turai ba hatta kasashen mu na Afrika ma sun bullo da haka, misali kasashe irin su Afirka ta Kudu da Ghana da kuma Senegal duk ’yan kasashensu da ke ketare suna yin zabe daga can.”\

Hakan abu ne mai kyau – Akilu Yabo

Daga Nasiru Bello, a Sakkwato

Akilu Yabo: “Alal hakika, bayar da damar yin zabe ga ’yan kasa mazauna waje wani abu ne mai kyau. Amma, bayar da irin wannan damar ga ’yan Najeriya, abu ne da bai dace ba. Dalili kuwa shi ne, an mayar da kasarmu  wata abar wasan yara; babu alkibla, ba mutunci, ba kuma bin doka da oda. Yaya aka kare da magudin zabe a nan cikin gida, bare ma a bayar da damar  gudanar da shi daga waje.”

Yana da kyau kwarai da gaske – Ambasada Shehu Wurno

Daga Nasiru Bello, a Sakkwato

Ambasada Shehu Wurno: “A gaskiya ya kamata duk inda dan kasa yake ya yi zabe wato ka zabi wanda kake so, rashin ba ka dama tauye hakkinka ne. Kuma hakan bai kamata ba saboda yadda yanzu muke karkashin mulkin dimukradiyya. Kuma wannan shirin  alheri ne ga mutanen da ke waje.”

Hakan ci gaba ne sosai – Alhaji Shehu Bakori

Daga Umar Rayyan, a Abuja

Alhaji Shehu Bakori: “Wato gaskiya wannan matakin ci gaba ne sosai saboda yadda zai ba da dama ga kowane dan Najeriya ya kada kuri’a , ba tare da la’akari da cewa yana nan gida ba ne. Amma mu babban fatanmu shi ne Ubangiji Ya ba mu shugabanni nagari, musamman ma saboda addu’armu  da muke yi ta Allah Ya zaunar da kasar nan lafiya.”

Ina tsoron matakin – Shazali Shu’aibu

Daga Umar Rayyan, a Abuja

Shazali Shuaibu: “Yadda ake maganar cewa ’yan Najeriya da ke ketare za su kada kuri’arsu abu ne mai kyau. Amma tsoronmu shi ne ka da a je a cika akwatunan zaben da kuri’un bogi. Ka ga a gaskiya wannan ita ce damuwata. Saboda yadda a cikin gida ma muke ganin magudin zabe da rana tsaka, karara, ballantana  kuma daga keatare. Muna dai fatan idan hakan ya tabbata, a yi komai tsakani da Allah.”