✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Adamawa ku taimaka wa Njabari

  Hausawa na Karin magana cewa juma’a da zai tayi kyau tun daga labara ke gane wa. Wannan maganan haka ta ke a hukumar Tara…

 

Hausawa na Karin magana cewa juma’a da zai tayi kyau tun daga labara ke gane wa. Wannan maganan haka ta ke a hukumar Tara kudin shiga na

Jihar Adamawa. Tun daga lokacin da aka bayar da labari cewa Gwamnan Jihar Adamawa Sanata Mohammed Umaru Jibrilla Bindow, ya amince da nada

Alhaji Hamman Adama Njabari, a matsayin sabon Shugaban hukumar tara kudin shiga na jihar Adamawa, jama’a ke ta cewa wannan nadin ya yi kyau saboda an samu haziki masanin makamar aiki tara kudi yanzu. Don haka, da kama aiki Alhaji Hamman Adama Njabari bai bata lokaci ba sai ya fara daidaita sahun ma’aikatan hukumar ta waje, kowa ya fahimci aiki sa sosai. Sanin makamar aiki ne ya bai wa Njabari damar tara kudin haraji yadda ya dace.

Shugaban bai tsaya nan ba, sai ya mayar da hankalin sa waje kirkiro hanyoyin samun kudi shiga kamar fitar da wata hanya biya kudin yin rajista na koyon tuka mota wanda da, ba a biya. Baya haka, Shugaban hukumar ya karkata hankalin sa wurin samar da ingattacen ofis, inda ma’aikata za su samu yin aikinsu sosai da so sai.

Yau, idan mutum ya shiga ofishin hukumar zai yi mamaki kwarai da gaske saboda ingancin wuri aiki, wanda Alhaji Hamman Adama Njabari ya yi hawansa mulki  kujerar Shugaban hukuman tara kudi shiga na Jihar Adamawa. Alhaji Hamman Adama Njabari, mutum ne wanda ke son bai wa kowa hakkinsa, musamman wajen kwazo da himma da mutum ya yi don samun ci gaba. Shugaban ba ya son wani babba ya danne hakkin wani karami. Gwani na gwanaye Hamman Adama Njabari, yana kokarinsa wajen gani duk kudin shiga na Jihar Adamawa ya shiga asusun jihar don gwamnatin ta samu kudi yin ayyuka don ci gaba jihar da al’umman baki daya.

Alhaji Hammanadama Njabari, ya dauki aniyar yin aiki don ci gaban Jihar Adamawa bisa amana da Gwamnan jihar ya ba shi. Don haka

ne ma ya fara da samar da kayayyakin aiki ga gundumumi ofishin tara kudi shiga da ke a Michika, Numan, Ganye da kuma Yola. Bisa haka ne ma ya gudanar da wasu canje-canjen hazikan ma’aikatan hukumar don samun biyan bukata wajen tara kudin shiga don gwamnati ta samu yi wa jama’a aiki.

Dole a yaba wa Gwamna Jihar Adamawa saboda zakulo irin wannan mutum gwani don jagoran  wannan hukumar. Su ma wanda suka yi takara da jarrabawa tare da shi sun cancanci yabo, musamman wadanda suka aiki tare a hukumar.

Su ma kananan ma’aikata da suke karkashinsa don goyon baya da suka ba shi hara ma ta kai ga samun wannan mukamin shugabancin hukumar gaba daya. Allah ya taya ka riko da kuma shugabanci bisa tsoronsa da kuma nuna adalci. Kuma ya kamata shugaban ya baya kowa hakkin sa daidai, tare  da bai wa kanana damar ci gaba, ta hanyar halartar bita da tarurrukan kara wa juna sani don sanin makamar aiki. dorewar managartan dabaru da wannan baean allah ya dauko  zai sa a samu ci gaba, musamman wurin tanadin samar da kudi a asusun gwamnati Jihar Adamawa.

Ma’aikatan hukumar ma ya kamata su ba da hadin kai ga shugaban don komai ya tafi da daidai wa daidaita. Hadin kai shi ne kadai abu da zai kai ga hukumar ta samu nasara don cimma nasara a kowane lungu. Wannan nadin gwani na gwanaye ta wurin zama shugaban hukumar tara kudin shiga na Jihar Adamawa ya yi. Kuma kowa ya kamata ya ba da gudunmuwaraa ga Alhaji Hammanadama Njabari. Al’ummar Jihar Adamawa masu kishin kasa, lallai mu had akai mu taimaka wa Alhaji Hamman Adama Njabari ya ci gari a wannan gagarumin aiki d ake gabansa.

Usman Santuraki ya rubuto makalarsa daga gida mai lamba biya, jambutu, Jimeta-Yola njihar Adamawa Usman Santuraki <[email protected]>