✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Boko Haram 16 da ‘yan gudun hijira 4 sun mutu a musayar wuta a Borno

Akalla mayakan Boko Haram 16 ne suka mutu a ba-ta-kashin da suka yi da sojoji a damboa

Akalla mutum 20 ne suka hallaka, ciki har da mayakan Boko Haram 16 lokacin da ‘yan ta’addan suka yi yunkurin kai hari wani sansanin sojoji dake kudancin jihar Borno da yammacin ranar Lahadi.

Maharan, a cewar rahotanni sun shiga garin na Damboa da misalin karfe 4:40 na yamma sannan suka bude wuta tare da kashe wasu ‘yan gudun hijira hudu, yayin da sama da mutum 10 kuma suka sami raunuka yayin musayar wutar.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta ce mayakan sun kaddamar da harin ne a kan sansanin sojojin, amma sakamakon tirjiyar da suka fuskanta, nan take aka hallaka 16 daga cikinsu.

Majiyar ta kara da cewa an shafe kimanin sa’o’i uku ana ba-ta-kashi, kafin daga bisani sashen sojojin sama na rundunar tsaro ta Operation Lafiya Dole su kawo wa rundunar kasa tallafi ta sama har aka sami nasara kan ‘yan ta’addan.

“Ina mai tabbatar maka da cewa ba a sami ko da mutum daya da ya mutu daga banagarenmu na sojoji ba. Duka rundunonin sama da na kasa sun yi namijin kokari gaskiya,” inji majiyar.

Kazalika, wani dan kungiyar kato-da-gora a yankin na Damboa, Hamisu Bakura, ya shaidawa Aminiya ta wayar salula cewa ‘yan ta’addan sun zo da motocin igwa sama da 20 sannan suka rika harbin kan mai uwa da wabi.

Ya ce, “Kowa kawai gudu yake domin ya tsira da rayuwarsa, wanda a nan ne mutum uku daga cikin wasu ‘yan gudun hijira suka mutu a musayar wutar, wani kuma ya mutu a asibiti, jimla mutum hudu kenan.

“Amma muna murna cewar an kashe da dama daga cikin ‘yan Boko Haram din. Maganar da muke da kai yanzu sai murna ake ta yi a garin Damboa,” inji Hamisu.